Jerin Kasashe 10 Masu Arhar Man Fetur a Watan Nuwamban 2024
Matsakaicin farashin man fetur a duniya ya kai N1,973.51 kan kowace lita wanda ya yi daidai da $1.117.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Sai dai, akwai bambanci mai girma kan wannan farashin na man fetur a tsakanin ƙasashen duniya.
Meyasa ake samun bambanci a farashin fetur?
Ƙasashe masu arziƙi suna da farashi mai tsada, yayin da ƙasashe masu fama da talauci da ƙasashen da suke haƙowa da fitar da man fetur, suke da farashi mai arha, cewar rahoton globalpetrolprices.com
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bambance-bambancen farashin da ake samu a ƙasashe, na faruwa ne sakamakon haraji daban-daban da kuma tallafin mai da gwamnatoci ke biya.
Ƙasashe masu arahar fetur
Ƙasar Iran ce ke kan gaba a jerin ƙasashe masu farashin man fetur mafi arha a watan Nuwamba, inda yake a $0.029 wanda ya yi daidai da N48.146.
Ga jerin ƙasashe 10 waɗanda ke da mafi ƙarancin farashin mai a cikin watan Nuwamban, 2024.
1. Iran
Iran tana da farashin man fetur mafi arha a duniya, wanda ya ke a $0.029 (N48.146) kacal kan kowace lita, rahoton tradingeconomics.com ya tababtar.
Wannan farashi mai arha yana nuna irin ɗumbin arziƙin man fetur na ƙasar, da kuma tallafin da gwamnati ke badawa da nufin samar da makamashi mai sauki ga ƴan ƙasar.
2. Libya
A ƙasar Libya, farashin man fetur yana a $0.031 kan kowace lita kwatankwacin N51.577, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta biyu mafi arharsa a duniya.
Arziƙin man fetur da ƙasar ke da shi da tsarin ba da tallafi na gwamnati, ya sanya ana samun fetur da arha a Libya.
3. Venezuela
Ƙasar Venezuela ta zo a matsayi na uku cikin ƙasashe masu arhar fetur, inda farashin yake a $0.035 (N58.910) kan kowace lita.
Arhar ta samo asali ne saboda ɗumbin albarkatun man fetur da yadda gwamnati ke kula da farashinsa.
4. Angola
Angola tana da farashin man fetur wanda yake a $0.329 (N553.055) kan kowace lita.
Ƙasar tana cin wannan gajiyar ne a matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen samar da mai a nahiyar Afirka.
5. Kuwait
Farashin man fetur a ƙasar Kuwait yana a $0.341 (N574.257) kan kowace lita a halin yanzu.
A matsayinta na ɗaya cikin manyan ƙasashe masu fitar da mai, ƙasar Kuwait tana da farashin fetur mai arha.
6. Egypt
Ƙasar Egypt ta zo matsayi na shida a cikin ƙasashen da ke da arhar fetur, inda farashin yake a $0.343 (N576.688) kan kowace lita.
Gwamnatin Egypt tana ba da tallafi domin farashin fetur ya yi arha a ƙasar akasin tsarin da ke gani yau a Najeriya.
7. Algeria
Ƙasar Algeria tana da farashin man fetur na $0.344 (578.873) kan kowace lita.
A matsayinta na ƙasa mai samar da iskar gas da fetur, Algeria na amfani da tallafi domin samar da makamashi mai araha ga ƴan ƙasarta.
8. Turkmenistan
Turkmenistan na sayar da man fetur kan farashin $0.428 (720.601) kan kowace lita.
Farashin man fetur a ƙasar bai da tsada sosai saboda tallafin da gwamnati ke biya.
9. Malaysia
A ƙasar Malaysia, farashin man fetur yana kai $0.460 (N775.026) kan kowace lita.
A matsayinta na babbar mai samar da man fetur da iskar gas a Kudu maso Gabashin Asia, ƙasar tana da farashi mai rahusa.
10. Kazakhstan
Ƙasar Kazakhstan ta zo ta 10 a cikin jerin ƙasashe masu arhar fetur, inda farashinsa yake a $0.490 (824.318) kan kowace lita.
Ƙasar wacce ke a yankin Asia ta Tsakiya, tana da farashi mai sauƙi na fetur domin amfanin mutanenta.
NNPCL ya daina shiga tsakanin IPMAN da Dangote
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin mai na NNPCL ya tsame kansa daga shiga tsakani a harkar kasuwancin man fetur a matatar Aliko Dangote.
Kamfanin ya dauki matakin domin gudun biyan raran kudi yayin da ya ke shiga tsakanin dillalan mai da matatar Dangote.
Asali: Legit.ng