Gwamnan Neja Ya Fara Biyan Albashin da Ya Fi na Sauran Jihohin Arewa Ta Tsakiya
- Ƙungiyar kwadago ta NLC ta yaba wa Gwamna Muhammad Umaru Bago kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Neja
- Ma’aikatan sun bayyana gwamna Bago a matsayin “shugaban da ke cika alkawari” saboda fara biyan albashin N80,000 a Nuwamba
- Kungiyar NLC yi kalaman yabo ga gwamnan ne saboda sabon albashin jihar da ya fara aiki ya fi na sauran jihohin Arewa ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Ƙungiyar NLC reshen Neja ta yaba wa Gwamna Muhammad Umaru Bago kan aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.
Shugaban NLC na Neja, Idris Lafene, ya bayyana godiyarsu ga gwamnan kan fara biyan ma'aikatan jihar N80,000 a watan Nuwamba.
Kwamared Idris Lafene ya yi wannan godiyar ne a yayin wata hirarsa da jaridar The Guardian a Minna, babban birnin jihar Neja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bago ya fara biyan albashin N80, 000
Kwamared Lafene ya ce aiwatar da sabon albashin a watan Nuwamba 2024 ya faranta wa ma’aikata rai tare da rage musu wahalhalun tattalin arziki.
Ya tuno lokacin da ake tattaunawar albashin inda Gwamna Bago ya bayar da umarnin cewa a tabbatar an aiwatar kafin ya bar jihar.
NLC ta ce biyan sabon albashin a Nuwamba ya sa ma’aikatan Neja sun samu karin kudi a albashinsu wanda ya fi na sauran jihohin Arewa ta Tsakiya.
Ma'aikata sun jinjinawa Gwamna Bago
Kwamared Lafene ya tabbatar da cewa ƙungiyar kwadago ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kula da walwalar ma’aikata a jihar.
Wasu ma’aikatan jihar sun yaba wa Gwamna Bago bisa wannan mataki, suna masu cewa shi shugaba ne da ke cika alkawari.
Ma’aikatan sun ce za su ninka ƙoƙarinsu wajen gudanar da aikinsu saboda goyon bayan da suke samu daga gwamnatin jijar karkashin Bago.
Bago ya fadi albashin ma'aikatan Neja
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnan Neja, Muhammed Umaru Bago ya amince da N80,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Umaru Bago ya sanar da sabon albashin ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da kungiyoyin kwadago a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng