Ma'aikata Za Su Cigaba da Jira, Gwamnan Zamfara Zai Fara Biyan Mafi Karancin Albashi a 2025
- Gwamnatin Zamfara da kungiyar kwadago watau NLC sun cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi na N70,000 a wata
- A wani taro da ya gudanar ranar Litinin, gwamnatin Dauda Lawal ta amince za ta fara biyan sabon albashin a watan Maris, 2025
- Kungiyar NLC reshen jihar Zamfara ta janye yajin aikin da ta shirya shiga saboda rashin aiwatar da dokar ƙarin albashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Gwamnatin Zamfara ta amince za ta fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi na N70,000 daga watan Maris, 2025.
Gwamnatin ta sa hannun kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ƴan kwadago kan aiwatar da dokar sabon albashi mafi kankanta na kasa.
Channels tv ta ruwaito cewa an cimma wannan matsaya ne ranar Litinin a taron da ya gudana tsakanin wakilan gwamnati da NLC a Gusau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Zamfara zai fara biyan N70,000
Taron ya kuma tattauna kan wasu ƙorafen ƙungiyar kwadago watau NLC ciki har da batun inganta walwala da jin daɗin ma'aikatan Zamfara.
Bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaban NLC reshen jihar, Kwamared Sani Haliru ya tabbatar da cewa sun fasa shiga yajin aikin da suka tsara.
Ƙungiyar NLC ta yabawa gwamnatin Zamfara
Ya yabawa gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal bisa yadda ta zaɓi tattaunawa da NLC kuma ta ɗauki lamarin walwalarsu da muhimmanci.
A rahoton Punch, Kwamared Sani ya ce:
"Idan kuka duba babu wani tsari na aiwatar da dokar ko wata yarjejeniya kafin yau amma yanzu ga shi mun sa hannu, shi kansa mai girma gwamna yana ofis yana jiran ya ji sakamakon wannan taro.
"Kafin yau raina ya ɓaci game da abubuwan da ke faruwa, na nemi mu zauna a tattauna amma a farko suka ce ba zai yiwu ba.
"Na ba da umarnin mu tafi yajin aiki amma yanzu ga shi sun dawo sun yi abin da ya kamata su yi tun farko, yanzu dai za mu kai rahoto ga hedkwatar NLC ta ƙasa."
Gwamnatin Zamfara ta damu da ma'aikata
Sakataren gwamnatin Zamfara, Abubakar Nakwada, ya bayyana cewa gwamna a shirye yake ya fara aiwatar da dokar ƙarin albashi.
Ya kuma bai wa ma’aikata tabbacin cewa gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin ta kulla alaka mai kyau da kungiyoyin kwadago.
Abubakar Nakwada ya kuma tabbatar da cewa za a fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 a watan Maris na 2025.
Ma'aikata sun shiga yajin aiki a jihohi
Rahoto ya zo cewa ma’aikata a wasu jihohin Arewa da Kudu sun fara yajin aikin mako guda domin neman aiwatar da sabon mafi karancin albashi
Ofisoshin gwamnati a jihohin da suka tafi yajin aikin da suka haɗa da majalisar dokoki, kotuna da ma’aikatu suna rufe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng