'Yan Kwadago Sun Fara Yajin Aiki a Jihohi 4 saboda Gaza Karin Albashin Ma'aikata
- Ma’aikata a wasu jihohin Arewa da Kudu sun fara yajin aikin mako guda domin neman aiwatar da sabon mafi karancin albashi
- Ofisoshin gwamnati a jihohin da suka tafi yajin aikin da suka haɗa da majalisar dokoki, kotuna da ma’aikatu suna rufe a yanzu
- A na shi bangaren, gwamnan jihar Ebonyi ya yi barazanar sallamar duk wani ma’aikacin da ya shiga yajin aikin cikin sa’o’i 72
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A ranar Litinin ma’aikatan gwamnati a jihohi huɗu na Najeriya da suka hada da Kaduna, Nasarawa, Ebonyi, da Cross River sun fara yajin aikin gargadi na mako daya.
Rahotanni na nuni da cewa yajin aikin ya samo asali ne daga gaza aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Daily Trust ta wallafa cewa ofisoshin gwamnati da suka haɗa da majalisar dokoki, kotuna da ma’aikatu sun kasance a rufe a Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin ƙwadago sun bayyana cewa yajin aikin ya zama dole ganin cewa gwamnatocin jihohi ba su cika alkawuran da suka ɗauka ba na karin albashi.
Ana yajin aiki a Kaduna da Nasarawa
A Kaduna, ofisoshin gwamnati da suka haɗa da sakatariyar jiha, kotuna da sauran wuraren aiki su na garkame sakamakon umarnin ƙungiyar ƙwadago.
A Nasarawa kuwa, Punch ta wallafa cewa shugaban NLC, Ismaila Okoh ya ce duk da alkawarin biyan N70,500 daga gwamnati, babu wata yarjejeniya da aka cimma a rubuce
Yajin aikin Ebonyi da Cross River
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya yi barazanar korar duk ma’aikacin da ya shiga yajin aikin cikin sa’o’i 72.
A Cross River kuwa, ƙungiyoyin ƙwadago sun yi watsi da sanarwar biyan N70,000 na mafi karancin albashi inda suka fara yajin aiki.
Shirin cigaba da yajin aiki a jihohi
A Calabar, babban birnin jihar Cross River ofisoshin gwamnati sun kasance a rufe yayin da 'yan ƙwadago ke shirin tattaunawa kan yanke shawarar ko za a tsawaita yajin aikin.
Kungiyoyin ƙwadago sun bayyana cewa matakin yajin aikin na nuni da aniyarsu ta tilastawa gwamnati biyan hakkokin ma’aikata da cika alkawuran da suka ɗauka.
NLC ta fasa shiga yajin aiki a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ke shirin yi kan mafi ƙarancin albashi ya samu cikas a Sokoto.
Ƙungiyar NLC reshen jihar Sokoto ta dakatar da shiga yajin aikin da aka shirya gudanarwa kan gaza biyan mafi ƙarancin albashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng