Kwanaki da Aurenta, Yar Kwankwaso Ta Saka Mahaifinta Alfahari, Aisha Ta Sha Yabo

Kwanaki da Aurenta, Yar Kwankwaso Ta Saka Mahaifinta Alfahari, Aisha Ta Sha Yabo

  • 'Yar Sanata Rabiu Kwankwaso ta yi fice a Jami'ar Nile da ke Abuja bayan zama fitacciyar daliba daga cikin sauran dalibai
  • Dr. Aisha Rabiu Kwankwaso ta zama gwarzuwa cikin daliban da suka kammala karatu a tsangayar karatun likitanci
  • Wannan na zuwa ne kasa da makwanni uku bayan daura auren Dr. Aisha da mijinta, Fahad Dahiru Mangal a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jagoran siyasar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya halarci bikin yaye daliban Jami'ar Nile da ke birnin Tarayya Abuja.

Daga cikin daliban da aka yaye akwai yar Sanatan mai suna Dr. Aisha Rabiu Kwankwaso wacce ta yi aure a yan kwanakin nan.

Kwankwaso ya taya 'yarsa murna kammala karatun likitanci
Sanata Rabiu Kwankwaso ya halarci bikin yayae dalibai ciki har da 'yarsa, Dr. Aisha. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Kwankwaso ya taya 'yarsa murna kammala jami'a

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X a jiya Litinin 2 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Yan Arewa sun hada kai babu bambanci, sun taso Barau Jibrin gaba kan kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya yi murna da Dr. Aisha ta zama gwarzuwar daliban gaba daya a tsangayar karatun likitanci a Jami'ar.

'Dan siyasar ya taya Dr. Aisha da mijinta, Fahad murna da sauran wadanda suka kammala karatu a Jami'ar ta Nile.

Dr. Aisha Kwankwaso ta zama gwarzuwar dalibai

"Ni da iyali na mun samu halartar bikin yaye dalibai a Jami'ar Nile domin taya 'yata Dr. Aisha Rabiu Kwankwaso murnar zama gwarzuwar daliba a tsangayar karatun likitanci."
"Ta samu maki mafi kyau a kwasa-kwasai guda biyar da ta yi yayin da aka karrama ta kan haka a Jami'ar."
"Ina taya Aisha da mijinta, Fahad da sauran wadanda suka kammala karatunsu murna, ina yi musu fatan alheri a rayuwarsu."

- Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso ya godewa al'umma bayan daurin aure

Kun ji cewa jagoran NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi magana karon farko bayan daura auren yarsa, Dr. Aisha da Fahad Dahiru Mangal.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 tana rufe, Gwamna ya bude wata babbar kasuwar dabbobi a Kaduna

Rabi'u Musa Kwankwaso ya mika godiya ga dukkan mutanen da suka taho Kano daga jihohi suka taya shi murnar bikin yarsa.

An daura auren Aisha Rabi'u Musa Kwankwaso da Fahad Dahiru Mangal ne a fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.