An Canza Wurin Daurin Auren Iyalan Ado Bayero da Barau kan Kudirin Haraji? An Gano Gaskiya

An Canza Wurin Daurin Auren Iyalan Ado Bayero da Barau kan Kudirin Haraji? An Gano Gaskiya

  • Kwanaki kadan kafin daurin auren iyalan Nasir Ado Bayero da Sanata Barau Jibrin, an canza wurin daurin auren daga Kano zuwa Abuja
  • Mutane da dama sun yi ta alakanta daukar matakin da cewa akwai siyasa a ciki duba da ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji
  • Sai da iyalan amarya sun fitar da sanarwa ta musamman domin fayyace gaskiya kan dalilin canza wurin auren zuwa birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Iyalan tsohon Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero sun yi martani kan dalilin canza wurin daurin aurensu da iyalan Sanata Barau Jibrin zuwa Abuja.

Iyalan sun musanta cewa akwai siyasa a musabbabin fasa auren tsakanin Maryam Ado Bayero da Jibrin Barau Jibrin a Kano.

Iyalan Nasir Ado Bayero sun fadi dalilin dage auren yaron Barau daga Kano zuwa Abuja
Alhaji Aminu Dan Agundi ya musanta alakar siyasa da dage auren iyalan Nasir Ado Bayero da Barau Jibrin. Hoto: @barauijibrin.
Asali: Twitter

An gano dalilin dage auren Barau a Kano

Kara karanta wannan

An kama mai taimakon 'yan bindiga da waya suna kira domin karbar kudin fansa

Sarkin Dawaki Babba na Kano, Alhaji Aminu Dan Agundi shi ya tabbatar da haka a jiya Litinin 2 ga watan Disambar 2024, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce babu zancen alaka tsakanin dage auren da kuma ce-ce-ku-ce da ake yi kan sabon kudirin haraji.

Dan Agundi ya ce bangaren iyalan amarya ne suka dauki matakin duba da al’adu ba tare da sa hannun gidan Sanata Barau ba.

“Dage auren ‘ya’yanmu da na Barau daga Kano zuwa Abuja bai da alaka da siyasa wanda iyalan amarya ne suka dauki wannan mataki babu hannun iyalan Sanata Barau.”
“Duba da al’adu, gidan amarya ne suke da ikon sauya wurin daurin aure sabanin yadda ake cewa iyalan Barau ne suka dauki matakin.”

- Aminu Babba Dan Agundi

Rokon Dan Agundi ga al'umma kan yada jita-jita

Daga bisani, Dan Agundi ya roki al’umma da su guji yada jita-jitar ba tare da sanin ainihin dalilin daukar matakin ba.

Kara karanta wannan

'A tafawa Barau': An sake yin rubdugu kan Rarara da ya saki wakar sanatan game da haraji

Ya bukaci al’umma da su kiyayi siyasantar da auren, ya ce aure wani abu ne na addini da ke da matukar muhimmaci da ba shi da alaka da siyasa.

Martanin yan Arewa kan auren dan Sanata Barau

Kun ji cewa an sanar da daurin auren dan Sanata Barau Jibrin da yar tsohon Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero a fadar Nassarawa.

'Yan Najeriya sun yi martani kan lamarin in awdasu suka sanya alheri yayin da wasu ke korafi kan fadar da aka zabi daura auren.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.