'Abin da Ya Sa Gwamnonin Najeriya Suka Bukaci Tinubu Ya Janye Kudirin Haraji'

'Abin da Ya Sa Gwamnonin Najeriya Suka Bukaci Tinubu Ya Janye Kudirin Haraji'

  • Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana asalin dalilin da ya sa gwamnonin jihohin Najeriya suka nemi a janye kudirin sauya fasalin haraji
  • Sule ya ce gwamnoni na son dakatar da kudirin ne saboda a sake tattaunawa su fahimci duk abin da ke ciki kafin a miƙawa majalisa
  • Gwamnan jihar Nasarawa ya ce waɗannan matakan da aka tsallake sune suka fi damun gwamnonin jihohi game da sabon kudirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce ba daidai ba ne a ce gwamnonin jihohi 36 na adawa da dokar sake fasalin haraji. 

Gwamna Sule ya ce shi da takwarorinsa na jihohin Najeriya ba adawa suke da kudirin ba, illa iyaka dai suna bukatar a zauna a fahimci juna kafin zartar da dokar.

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamnan Nasarawa ya yi karin haske game da matsayar gwamnoni 36 kan kudirin harajin Tinubu Hoto: Abdullahi A Sule
Asali: Facebook

Abdullahi Sule ya bayyana haka ne a taron muhawara da gidan talabijin na Channels ya shirya ranar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2023.

Kara karanta wannan

"Majalisa za ta amince da kudirin haraji kuma babu abin da zai faru," Sanata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin 36 sun nemi a janye kudirin haraji

Gwamnan ya yabawa kudirorin guda huɗu da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar amma ya ce akwai wasu kulle-ƙulle da ke bukatar a warware su.

"Kamar batun ƙara kason da ake warewa inɗa suka fi tara harajin VAT daga kashi 20 zuwa 60, na ji daɗi Taiwo ya ce an canza, har da wuraren da aka fi cinikin kaya."
"Akwai batutuwan da gwamnoni suka zaƙulo, mu abin da muke cewa, ku janye kudirin nan, mu zauna a tattauna, mu fahimci duk abin da ke ciki," in ji Sule.

Gwamnonin Najeriya sun faɗi bukatarsu

Gwamna Abdullahi Sule ya kara da cewa ko wannan taron da Channels tv ta shirya kamata ya yi a gudanar da shi tun kafin miƙa kudirin ga majalisa.

A cewarsa, da tun farko kwamitin sauya fasalin haraji da Taiwo Oyedele ke jagoranta ya ɗauki waɗannan matakan kuma an fito da komai fili da babu mai sukar kudirin.

Kara karanta wannan

Kudirin sauya fasalin harajin Tinubu ya ƙara gamuwa da cikas a jihar Kano

Sule ya ce wannan rashin cikakken bayani kan kudirin da saurin miƙa shi majalisa ne babbar damuwar gwamnonin Najeriya.

Dalilin gwamnonin Arewa na adawa da kudirin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana dalilin gwamnonin Arewa na son dakatar da ƙudirin haraji.

Zulum ya bayyana cewa gwamnonin na buƙatar lokaci domin yin shawarwar kan ƙudirin wanda ke gaban majalisar dattawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262