"Majalisa Za Ta Amince da Kudirin Haraji Ko Sama da Ƙasa Za Su Haɗe," Sanata
- Sanata Seriake Dickson mai wakiltar Bayelsa ta Yamma ya ce majalisa za ta amince da sabon kudirin haraji na Bola Tinubu
- Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya ce ko sama da ƙasa za su haɗu sai sun zartar da dokar sauya fasalin haraji kamar yadda aka yi a dokar PIA
- Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ciki har da gwamnoni suka nuna adawa da sabon tsarin harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da muhalli da sauyin yanayi, Seriake Dickson (PDP, Bayelsa ta Yamma), ya ce za su zartar da kudirin gyara haraji.
Sanata Dikson ya ce kamar yadda majalisar ta amince da dokar ma fetur watau PIA, haka za ta zartar da kudirin sauya fasalin haraji ko sama da ƙasa za su haɗe.
Majalisa za ta amince da kudirin haraji
Seriake Dickson, tsohon gwamnan jihar Beyelsa ya bayyana hakan ne a wata hira da ƴan jarida a Abuja yau Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce duk da sukar da ake wa kudirin daga kowane ɓangare, majalisar tarayya za ta amince da shi ko ma mai zai faru ya faru.
A ranar 3 ga Oktoba, 2024, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika wa Majalisar dokoki ta ƙasa wasu kudirori hudu na sake fasalin haraji.
Sai dai ‘yan Najeriya da suka hada da gwamnoni, sarakuna, kungiyoyin farar hula, ‘yan majalisar tarayya da sauransu sun yi fatali da kudirin dokar.
"Za mu zartar da kudirin haraji" - Dickson
Da yake tsokaci kan surutun da ake ta yi, Sanata Dickson ya ce:
"A baya an zartar da dokar mai watau PIA, kaso 10% muka nemi a ware mana kamar yadda da Marigayi Yar’adua ya kawo, amma ƴan majalisa suka rage shi zuwa kashi 3%, ba abin da ya faru.
"Don haka zamu amince da wannan kudirin sauya fasalin harajin ko sama da ƙasa za su haɗe. Majalisar dattawa ta amince a yi wa kudirin karatu na 2, za a fara sauraron ra'ayoyin jama'a."
Fadar shugaban ƙasa ta maida martani
A wani labarin, an ji cewa Fadar shugaban kasa ta nuna rashin jin dadin yadda wasu a kasar nan ke sukar kudirin harajin da gwamnati ta bijiro da shi.
Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kafafen yada labarai, Sunday Dare ya bayyana cewa kudurin na da muhimmanci.
Asali: Legit.ng