Kudirin Haraji: Lauya Ya Fallasa Babban Burin Legas da Aka Kudiri Niyyar Tabbatarwa
- Fitaccen lauya, Barista Bulama Bukarti ya fadi gagarumin illar da kudurin harajin Bola Tinubu zai yi ga Arewa
- Ya ce ba tun yanzu ba, Tinubu da mukarrabansa ke kokawa kan tsarin rabon haraji da gwamnati ke yi
- Lauyan ya fallasa matsalar da kudurin ya kunsa ga sauran jihohi, banda Legas da Ribas da za su ci moriyarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Lauya mai kare hakkin dan Adam, Barista Bulama Bukarti ya tona yadda gwamnatin Bola Tinubu ke kokarin tabbatar da abin da ta gaza cimmawa a lokacin da su ke rike da kambun gwamnatin Legas.
Barista Bulama Bukarti ya yi wannan tonon silili ne a lokacin da gwamnati ta dage a kan majalisa ta amince da sabon kudurin haraji, wanda ake hasashen zai cutar da Arewa.
Barista Bulama Bukarti ya fadi haka ne ta cikin shirin Fashin Baki, inda su ka tona abin da kudurin ke nufi, bayan an kullo ta tun a zamanin Tinubu na gwamnan Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu za ta cimma manufar Legas?
Barista Bulama Bukarti ya ce kusoshin gwamnatin Tinubu a zamaninsa na gwamnan Legas, su ne aka zuba a sashen da zai bijiro da dokar haraji a wannan gwamnatin.
"Sun fara rigimar nan tun Tinubu ya na gwamna, Antoni Janar na yanzu na Najeriya, shi ne lauya jihar Legas a wancan lokacin.
Kuma Ministan kudin Najeriya na yanzu, shi ne kwamishinan kudi na jihar Legas a wannan lokacin."
- Barista Bulama Bukarti
Ya yi zargin cewa su na son amfani da ikon na shugabancin kasa domin cimma abin da su ka gaza samu a shekarun baya na mallakawa Legas kason kudin harajinta.
An fadi illolin ƙudurin harajin Tinubu
Wani Abubakar Umar Muhammad ya wallafa bidiyon wani sashe na shirin Fashin Baki a shafinsa na Facebook, inda aka zayyano wasu daga cikin Illolin kudurin haraji.
Barista Bulama Bukarti ya ce jihohin Arewa kamar su Bauchi, Yobe da Jigawa, ba za su iya rika biyan ma'aikatansu albashi ba idan kudirin ga tabbata zuwa doka.
An yi fatali da kudirin harajin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa wasu daga cikin shugabannin Arewacin kasar nan sun bayyana rashin gamsuwa da yadda gwamnatin Bola Tinubu ke kokarin tilasta kudirin haraji.
Daga cikin jagororin akwai gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, da wasu 'yan majalisa da su ka fito daga jihar, inda su ka ce ba za su amince da sabon kudurin harajin ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng