Ma'aikatan Lafiya Za Su Tsunduma Yajin Aiki a Arewa, Sun Kafawa Gwamna Sharadi
- Ma’aikatan lafiya sun nemi gwamnatin Zamfara ta biya su bashin albashi da alawus na wata da suke bi ko su shiga yajin aiki
- Rashin daidaito a cikin biyan albashin watan Oktoba da Nuwamba ya sa wasu ma’aikata suka bar aiki, duk da korafe-korafen su
- Ma'aikatan sun nemi a kafa kwamitin gudanarwa da tabbatar da biyansu alawusa-alawus domin inganta aikin lafiya a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Ƙungiyar ma’aikatan lafiya a asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau, sun yi kira ga gwamnatin Zamfara ta biya basussukan albashinsu.
Sun bayyana cewa suna bin bashin albashin wata shida daga Yuni zuwa Nuwambar 2024 bisa sabon tsarin albashi na CONHESS da suke a kai.
Ma'aikata na bin gwamanti bashin albashi
Shugaban kungiyar, Kwamared Sani Rabi’u, ya ce suna buƙatar a biya su dukkanin alawus na karin matsayi, kira zuwa aiki da na haɗari, a cewar rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar ta gano tasgaro a cikin albashin watan Oktoba da Nuwamba 2024 da gwamnati ta biya wanda ya haɗa da zabtarewa da kuma kin aiwatar da karin albashin wasu.
Kungiyar ta ce ce ma’aikatan asibitin sun rasa alawus ɗin da ya kamata su samu tun lokacin da aka kafa asibitin a birnin Gusau.
Zamfara: Ma'aikatan lafiya sun fara ajiye aiki
Kwamared Sani ya ce gwamnati ta rage albashin wasu ma'aikatan lafiya maimakon kara masu, wanda hakan ya sa wasu kwararrun ma’aikata ajiye aikin.
Duk da tarin korafe-korafe da ganawa da hukumomi, kungiyar ta ce gwamnati ba ta gyara wannan matsalar a cikin albashin watan Nuwamba ba.
Shugaban kungiyar ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da aiwatar da biyan alawus na karin matsayi, kira zuwa aiki da na haɗari bisa tsarin CONHESS.
Ma'aikatan lafiya za su shiga yajin aiki
Ya ce akwai buƙatar dawo da ikon cin gashin kai na asibitin tare da kafa kwamitin gudanarwa domin inganta aikin da ma'aikatan ke yi.
Rahoton TVC360 ya ruwaito kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta aiwatar da karin girma ga ma’aikatan da suka cancanta tun da daɗewa.
Sun ce idan gwamnati ba ta ɗauki matakin aiwatar da waɗannan buƙatun ba, za su shiga yajin aiki nan ba da daɗewa ba.
Jihohi 4 sun janye daga yajin aikin NLC
A wani labarin, mun ruwaito cewa yajin aikin da NLC ke shirin shiga a Disambar nan ya gamu da cikas yayin da ma'aikatan wasu jihohi suka janye jikinsu.
Jihohin da suka hada sda Imo, Sokoto da sauransu sun bayyana yarjejeniyar da suka cimma wa da gwamnoninsu kan sabon albashi na N70000.
Asali: Legit.ng