Sanatan da ba Musulmi ba Ya Gwangwaje Mahaddatan Kur'ani da Kyaututtuka

Sanatan da ba Musulmi ba Ya Gwangwaje Mahaddatan Kur'ani da Kyaututtuka

  • An gudanar da rufe gasar karatun Al-Kur’ani mai girma karo na 39 a karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa
  • Sanata Ishaku Abbo, wanda ba Musulmi ba ne ya ba da kyautar Keke Napep ga wadanda suka lashe gasar a matakai biyu
  • Taron ya samu goyon bayan Sarkin Demsa kuma manyan baki da suka hada da Atiku Abubakar sun shaida rufe gasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - A ranar Asabar da ta gabata aka gudanar da gagarumin taron rufe gasar karatun Al-Kur’ani mai girma a karamar hukumar Demsa.

Gasar ta hada mahaddata al-Kur'ani daga kanan hukumomin jihar inda aka fafata daga izifi biyu zuwa izifi 60.

Abbo I
Sanata Abbo ya ba mahaddatan Qur'ani Keke Napep. Hoto: Ishaku Abbo
Asali: Facebook

Manyan baki sun halarci taron daga wurare daban-daban kamar yadda Sanata Ishaku Abbo ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Yan Arewa sun hada kai babu bambanci, sun taso Barau Jibrin gaba kan kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Abbo ya ba mahaddatan Kur'ani kyauta

Sanata Ishaku Abbo, wanda ba Musulmi ba ne ya ba da kyautar Keke Napep guda biyu a matsayin yabo ga wadanda suka yi nasara a matakin izifi 60 da fassara da karatu zalla.

Sanata Abbo ya yi kyautar ne da nufin karfafa gwiwar matasa wajen neman ilimin addini da kuma inganta hadin kan al’umma.

Taron ya samu goyon bayan masarautar Demsa karkashin jagorancin sarkin Demsa, mai martaba Hamma Batta wanda shi ma ba Musulmi ba ne.

Bakin da suka halarci gasar Kur'ani

Daga cikin fitattun baki da suka halarci gasar akwai Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar da shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Haka zalika akwai mataimakin shugaban cocin LCCN, Bishop Bartholomew da sauran sarakunan gargajiya daga Adamawa da Gombe da manyan malamai.

A bidiyon da Atiku Abubakar ya wallafa a Facebook, ya yabawa sarkin Demsa da mutanen masarautar bisa hadin kai da suka bayar yayin gasar.

Kara karanta wannan

Dokar haraji: Sanatocin Arewa sun yi ganawar sirri bayan kudirin ya tsallake karatu na 2

Ganduje zai kai mahaddatan Kur'ani Hajji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi goma ta arziki ga wadanda suka lashe gasar karatun Alkur'ani a jihar Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mahaddatan Alkur'anin sun samu kyaututtukan da suka hada da kujerun Hajji da abubuwan hawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng