Ana Rikita Rikitar Kudirin Haraji, Bankin CBN Zai Sallami Ma'aikata 1,000

Ana Rikita Rikitar Kudirin Haraji, Bankin CBN Zai Sallami Ma'aikata 1,000

  • Bincike ya tabbatar da cewa babban bankin Najeriya (CBN) zai yi ritaya ga ma’aikata 1,000 kafin karshen wannan shekarar
  • Rahotanni daga babban bankin sun tabbatar da cewa CBN zai kashe sama da Naira biliyan 50 a matsayin biyan kudin ritaya ga ma’aikatan
  • Hakan na cikin tsarin da hukumar gudanarwar CBN karkashin jagorancin Olayemi Cardoso ta dauko na rage yawan ma’aikata kafi karshen 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN ya fitar da tsarin ba ma'aikata damar yin ritaya kafin lokacin gama aiki.

A karkashin shirin EPP da bankin CBN ya fitar, ma'aikata za su samu makudan kudi da za su je su ci gaba da rayuwa da su.

bankin CBN
Bankin CBN zai sallami ma'aikata 1,000. Hoto: Bayo Onanuga|Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa babban bankin zai kashe kudi sama da Naira biliyan 50 wajen sallamar ma'aikatan.

Kara karanta wannan

Kudirin sauya fasalin harajin Tinubu ya ƙara gamuwa da cikas a jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin CBN zai sallami ma'aikata 1,000

Babban bankin Najeriya ya fara shirin sallamar mutane kimanin 1,000 daga cikin ma’aikatansa.

An gano cewa matakin ritayar ma’aikatan, wanda zai hada da biyan kudin ritaya na cikin wani bangare na tsare-tsaren inganta tsarin aiki na bankin.

Wata takardar sanarwa da aka fitar kwanan nan ta nuna cewa an ba ma'aikatan damar yin ritaya ne a karkashin shirin EPP.

CBN: Ma'aikata sama da 800 sun nemi ritaya

Rahotanni daga cikin bankin sun bayyana cewa akalla ma’aikata 860 daga sassa daban-daban sun riga sun nemi shiga cikin shirin EPP.

Wani daga cikin ma'aikatan ya bayyana cewa ya yi aikin shekaru hudu a bankin kuma ana shirin sallamarsa da kudi tsakanin Naira miliyan 92 zuwa Naira miliyan 97.

Sharadin ajiye aiki a bankin CBN

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa a yayin da ma'aikata ke ribibin cika fom domin ajiye aiki a bankin, CBN ya fitar da gargadi.

Kara karanta wannan

Zulum ya kaddamar da katafariyar tashar jirgin kasa ta farko a Arewa.

Bankin ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi rajista ba zai iya canza ra'ayinsa ba bayan ya kammala cika fom din ajiye aiki.

Bankin CBN ya fara cire haraji a Opay

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara cire N50 kan duk wani kudi da aka turawa masu amfani da bankunan intanet da ya haura N10,000.

Tuni dai bankunan intanet irinsu Opay da Moniepoint suka bayyana cewa sun fara karbar kudin harajin kuma za su tura su kai tsaye ga FIRS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng