Fadar Shugaban Kasa Ta Dauki Zafi kan Zazzafar Adawa da Kudirin Haraji daga Arewa
- Fadar shugaban kasa ta nuna rashin jin dadin yadda wasu a kasar nan ke sukar kudirin harajin da gwamnati ta bijiro da shi
- Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kafafen yada labarai, Sunday Dare ya bayyana cewa kudurin na da muhimmanci
- Ya shawarci masu adawa da kudurin da su amince a zauna da su, su fahimci amfanin kudurin a maimakon sukar sa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT Abuja – Fadar shugaban kasa ta karyata cewa kudurin harajin da shugaban Bola Ahmed Tinubu ya bijiro da shi na da illa ga Arewa.
Wannan na zuwa bayan gwamnoni da wasu daga cikin ‘yan majalisa da su ka fito daga Arewacin kasar nan sun soki sabon kudurin.
Hadimin shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Sunday Dare ya wallafa a shafinsa na X cewa, yan yi wa kudurin gurguwar fahimta.
Gwamnati ta fadi amfanin kudurin haraji
Sunday Dare ya bayyana cewa kudurin harajin Bola Ahmed Tinubu za ta amfanar da dukkanin mazauna Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa matukar majalisa ta amince da kudurin ya zama doka, zai zama guda daga cikin manyan dokokin da kasa a wannan lokaci.
Kudurin haraji: Gwamnati ta nemi hadin kai
Fadar shugaban kasa ta bayyana takaicin yadda wasu manya a kasar nan ke kokarin kawo tasgaro da kudirin harajin gwamnati.
Sanarwar da Sunday Dare ya fitar ta ce;
“Kamata ya yi mu yi aiki tare wajen inganta wannan doka, domin jama’a su ci moriyarsa.”
Sanarwar ta kara da cewa;
"Tattaunawa, ba adawa ba; muhawara, ba zargi ba, za su kai mu ga mafita da za su amfani kowa. Wannan shi ne abin da Shugaban Ƙasa ya tsaya a kai."
Ya shawarci masu adawa da kudurin da su zauna a tattauna, tare da fahimtar kudurin domin amfanin kasa baki daya.
'Yan majalisa sun yi watsi da kudirin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa wasu daga cikin 'yan majalisar da su ka fito daga Kano sun yi duba na tsanaki kan batun kudurin harajin da gwamnatin tarayya ta gabatar gaban majalisa.
'Yan majalisar da su ka tattauna sun samu jagorancin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, sannan sun bayyana matsayarsu na cewa ba za su amince da kudurin da zai cutar da al'umma ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng