Tinubu: 'Yan Majalisun Arewa Sun sa an Dakatar da Muhawara kan Kudirin Haraji
- Majalisar Wakilai ta Najeriya ta dage tattaunawa kan kudirin gyaran haraji bayan samun matsin lamba daga Arewa
- Sanarwar majalisar ta ce dagewar ta biyo bayan bukatar kara yin shawarwari da masu ruwa da tsaki ne a kan kudirin
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dage kan amincewa da kudirin duk da adawar da ake yi a kansa daga Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta sanar da dage tattaunawa kan kudirin gyaran haraji da aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 3 ga Disamba.
Matakin ya biyo bayan matsin lamba daga gwamnonin Arewacin Najeriya da wasu 'yan majalisar dokoki daga yankin.
Rahoton Punch ya nuna cewa gwamnonin Arewa da wakilan yankin sun nuna rashin amincewarsu da kudirin, tare da bukatar neman karin shawarwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar dakatar da tattaunawar ta fito ne daga ofishin Sakataren Majalisar wakilai, Dr Yahaya Danzaria a ranar 30 ga Nuwamba.
Dalilin dakatar da tattauna kudirin haraji
Takardar da sakataren majalisar ya fitar ta nuna cewa an dage zaman ne domin bai wa majalisar damar gudanar da karin shawarwari da masu ruwa da tsaki.
“Mun yi haka ne don tabbatar da an samu fahimtar juna daga kowane bangare,”
- Hon. Yahaya Danzaria
'Yan majalisa 73 daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna rashin goyon bayansu ga kudirin, ciki har da 'yan majalisa 48 daga Arewa maso Gabas da 24 daga Kano.
The Cable ta wallafa cewa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, ya goyi bayan dakatar da tattaunawar.
Yaushe majalisa za ta tattauna kudirin haraji?
Majalisar ta bayyana cewa sabon lokacin tattaunawar zai kasance nan gaba, inda za a bayar da sanarwa ga mambobin majalisar da sauran masu ruwa da tsaki.
Lamari haraji na ci gaba da jan hankalin jama’a musamman daga Arewacin Najeriya da ake adawa da kudirin sosai.
Tinubu zai ruguza Arewa inji Bukarti
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake ta magana kan sabon kudirin haraji da Majalisar Tarayya ta yi zama a kai, Bulama Bukarti ya magantu.
Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana irin illar da kudirin harajin zai yi wa tattalin arzikin Arewa inda ya ce za a nakasa yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng