Zuwan Tinubu Faris: Najeriya ta Kulla Yarjejeniyar Ma'adanai da Faransa
- Najeriya da Faransa sun amince su yi aiki tare don inganta ma’adanai masu muhimmanci kamar su tagulla
- Yarjejeniyar ta kunshi hadin gwiwa kan bincike, horo, da musayar dalibai don sauya fasaha da kwarewa
- Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen rage illar hakar ma’adanai kan muhalli da gyara ramuka da aka bari a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
France - Najeriya da Faransa sun cimma matsaya kan hadin gwiwa domin bunkasa darajar ma’adanai masu muhimmanci.
Yarjejeniya ta kunshi cigaban fasahar makamashi mai tsafta ta hanyar inganta amfani da ma’adanai irin su tagulla da sauransu.
Jami'in yada labarai a ma'aikatar muhalli ta kasa, Segun Tomori ya wallafa a X cewa yarjejeniyar za ta bayar da damar kasuwanci a fannin ma’adanai a tsakanin kasashen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya vs Faransa: Amfanin yarjejeniyar ma'adanai
An bayyana cewa yarjejeniyar za ta ba da fifiko wajen rage illar da hakar ma’adanai ke yi wa muhalli.
Punch ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce aikin hadin gwiwar zai taimaka wajen gyara wuraren hakar ma'adanai da aka bari a Najeriya.
Ministan ma'adanai, Dr Dele Alake, wanda ya sanya hannu a madadin Najeriya ya ce matakin zai taimaka wajen kawo ci gaba mai dorewa a fannin ma’adanai.
Za a horas da dalibai a fannin ma'adanai
Yarjejeniyar ta kunshi musayar dalibai da horo tsakanin Najeriya da Faransa domin bunkasa kwarewar ma’aikata a bangaren ma’adanai.
Haka zalika, za a gudanar da taron karawa juna sani da horo akai-akai domin kara ingancin gudanarwa a fannin ma'adanai.
Yarjejeniyar ma'adanai za ta daga darajar Najeriya
Ministan Ma’adanai, Dr. Alake ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babbar dama ga gwamnatin Tinubu don kara wa Najeriya daraja a duniya.
Ana kuma sa ran yarjejeniya za ta inganta yawan ma’adanai da za a samar, tare da tabbatar da cewa duk wani aiki a fannin yana amfani da ka’idojin kasa da kasa.
Tinubu za tafi Afrika ta Kudu daga Faransa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron BNC na 11 tare da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa a Cape Town.
Taron zai mayar da hankali kan batutuwa daban-daban da suka shafi siyasa, tattalin arziki, tsaro, da kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Asali: Legit.ng