Rigimar Sarauta Ta Dauki Sabon Salo a Arewa, an Maka Sarki da Gwamna a Kotu

Rigimar Sarauta Ta Dauki Sabon Salo a Arewa, an Maka Sarki da Gwamna a Kotu

  • Rigimar sarauta ta sauya salo a jihar Kwara bayan mazauna Kajola sun yi korafi kan nadin basarake da suke ganin an saba ka'dar a nadin
  • Mazauna yankin Kajola da ke karamar hukumar Ero sun maka gwamnatin jihar a kotu kan kakaba masu sabon sarki
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin kakaba sarkin duk da ana cigaba da shari'a a kotu da ba a kammala ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Wasu mazauna Kwara sun maka gwamnatin jihar a kotu kan rigimar sarauta da ta ki ci ta ki cinyewa.

Al'mmar Kajola da ke karamar hukumar Ero a jihar sun yi barazanar shiga kotu da gwamnatin kan kakaba basarake.

An maka gwamna a kotu kan rigimar sarauta
Wasu mazauna jihar Kwara sun maka Gwamna a kotu kan kakaba musu sarki. Hoto: Legit.
Asali: UGC

Nadin sabon sarki ya jawo rigima a Kwara

The Guardian ta ce mazauna yankin sun dauki matakin ne duba da kakaba sarkin da aka yi wanda ake cigaba da tababa kan sarautar a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun je daukar fansar kashe abokin Sububu, an hallaka su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An maka sabon sarkin mai suna Prince Jide Kahinde da wasu mutane biyar a kotu kan kiran kansu masu nadin sarauta.

Ana zargin sun ayyana kansu masu nadin sarauta domin samun damar nadin Prince Kahinde kan kujerar sarautar.

Wadanda ke korafi kan nadin sabon sarki

Masu korafin sun hada da Princes Orishatuyi AbdulRoheem da Adeniyi Akanbi da AbdulSalam Abdul Azeez da Olayemi Oladipupo da Yusuf Adio.

Dukan masu korafin sun fito ne daga gidan sarauta na Idofin a garin Ekiti da suke ganin nadin sarkin zai sauya shari'ar da ke gaban kotun.

Masu korafin sun yi zargin cewa matakin nada sarkin ya saba ka'idoji da kuma al'adun nadin sarauta a jihar.

Gwamna Okpebholo a rushe masarautu a Edo

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Edo ta dauki wasu muhimman matakai kan sababbin masarautu da wata cibiyar al'adu.

Gwamna Monday Okpebholo shi ya dauki matakin inda ya dawowa Oba na Benin, Oba Ewuare II martabarsa da yake da shi a baya.

Wannan na zuwa ne bayan kirkirar sababbin masarautu da tsohuwar gwamnatin Godwin Obaseki ta yi a zamaninta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.