Yan Ta’adda Sun Je Daukar Fansar Kashe Abokin Sububu, an Hallaka Su
- Wasu yan bindiga da dama sun gamu da ajalinsu bayan sun je daukar fansar kisan jagoransu da aka kashe tun a watan Satumba
- Maharan sun ci karo da matsala ne a Unguwar Galadima da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara
- Yan ta'addan sun durfafi yankin da asuba ana shirin salla inda al'umma da yan banga suka farmake su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Yan bindiga da dama sun rasa rayukansu yayin wata arangama da yan banga a jihar Zamfara.
Yan bindigan sun kai harin ne domin daukar fansa bayan kisan jagoransu, Sani Black a watan Satumbar 2024.
Zamfara: An hallaka yan bindiga da dama
Premium Times ta ce Sani Black ya kasance na kusa da marigayi kasurgumin dan ta'adda, Halilu Sububu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a Unguwar Galadima da ke karamar hukumar Maru a yau Lahadi 1 ga watan Disambar 2024.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun iso yankin ne ana sallar asuba domin daukar fansar kisan Sani Black.
Lamarin ya tilasta maharan barin makamansu yayin da yan banga da al'ummar gari suka tunkare su.
Yan bindiga sun kai harin daukar fansa
"Maharan sun zo da misalin karfe 5.00 na safe lokacin ana shirin gudanar da sallar asuba, sun shiga yankin ne domin daukar fansar kisan Sani Black."
"Wannan shi ne karo na biyu da maharan ke kawo hari tun bayan da yan banga suka hallaka Black a watan Satumbar 2024."
"Abin farin ciki al'ummar yankin da yan banga sun kare kansu inda suka hallaka yan ta'addan da dama da kwace makamai masu yawa daga gare su."
- Cewar wata majiya
Fada ta barke tsakanin yan banga da yan ta'adda
A baya, kun ji cewa rahotanni sun tabbatar kazamar fada ta barke tsakanin yan banga da kuma yaran Bello Turji.
An yi arangamar a yankin Fadamar Tara da ke jihar Zamfara inda yan ta'addan suka yi kokarin kwace iko a yankin.
Sai dai yan banga sun kawowa al'ummar yankin da manoma dauki saboda kare mutane da ke rayuwa a wurin.
Asali: Legit.ng