'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mutane Masu Yawa Ciki Har da Jariri a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mutane Masu Yawa Ciki Har da Jariri a Zamfara

  • Ƴan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Kungurki da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara a yankin Arewa maso Yamma
  • Maharan sun yi awon gaba da mutane 13 a harin wanda suka kai a cikin daren ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamban 2024
  • Daga cikin mutanen da ƴan bindigan suka sace har da wani ɗan ƙaramin jariri da mahaifiyarsa, sannan suka kashe wani dattijo a yayin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai wani mummunan hari a jihar Zamfara a daren ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamban 2024.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Kungurki da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun yi ta'asa, sun hallaka jami'in dan sanda har lahira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Zamfara

Ƴan bindigan a yayin harin sun kashe wani dattijo tare da yin awon gaba da mazauna garin mutum 13, ciki har da jariri ɗan wata biyu da mahaifiyarsa.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyen ne a cikin duhu, inda suka riƙa harbe-harbe akai-akai domin sanya tsoro a zukatan mazauna ƙauyen.

Ƴan bindiga sun fasa shaguna

Baya ga sace mutanen, ƴan bindigan sun yi sata a shaguna da dama, inda suka kwashe kayayyakin abinci, kayan gida, da sauran kayayyaki masu amfani.

Ƴan bindigan sun riƙa tafiya cikin sanɗa, sannan suka tattara waɗanda suka sace suka tafi da su zuwa cikin dajin da ke kusa.

"Wannan abu ne mai ban tsoro. Sun kama mata, yara, sai kuma wani dattijo da aka kashe."

- Wani mazaunin ƙauyen

Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Hare-haren da aka kai ta sama a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, ya yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng