Mafi Karancin Albashi: NLC Ta Fadi Matsayarta kan Shiga Yajin Aiki a Sokoto
- Yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ke shirin yi kan mafi ƙarancin albashi ya samu cikas a Sokoto
- Ƙungiyar NLC reshen jihar Sokoto ta dakatar da shiga yajin aikin da aka shirya gudanarwa kan mafi ƙarancin albashi
- Shugaban ƙungiyar na jihar, ya bayyana cewa sun gamsu da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da gwamnati za ta fara a watan Disamban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Sokoto ta dakatar da shiga yajin aiki.
Ƙungiyar NLC a Sokoto ta fasa shiga yajin aikin da ta shirya yi kan aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Shugaban ƙungiyar NLC na jihar, Kwamared Abdullahi Aliyu Jungle ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ƙarshen mako, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa sabon albashin wanda za a fara biya a watan Janairun 2024, zai amfani ma’aikata na gaskiya da malaman makaranta a faɗin jihar, rahoton Vanguard ya tabbatar.
NLC na goyon bayan yarjejeniya da gwamnati
Abdullahi Aliyu Jungle ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga yarjejeniyar da aka cimmawa da gwamnatin jihar.
Ya jaddada cewa aiwatar da mafi ƙarancin albashi ya yi daidai da manufar bunƙasa ci gaba a jihar.
"Ƙungiyar NLC reshen jihar na goyon bayan aiwatar da mafi ƙarancin albashin N70,000 da gwamnati jiha ta sanar daga watan Janairun 2025."
“Za kuma mu taimakawa gwamnati wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi ko da hakan yana nufin gudanar da aikin tantancewa, domin tabbatar da cewa ma’aikata na gaske ne kawai za su ci gajiyar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000."
- Abdullahi Aliyu Jungle
NLC za ta shiga yajin aiki a Jigawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar NLC reshen Jigawa ta ayyana yajin aikin sai baba ta gani kan gazawar gwamnatin jihar na aiwatar da mafi karancin albashin N70,000 da aka amince da shi.
Wata sanarwa daga Sunusi Alhassan (NLC) da Bashir Tijjani Abubakar (TUC) ta umarci ma'aikatan jihar da su shirya tsunduma yajin aikin.
Asali: Legit.ng