Bayan kusan Shekaru 20, za a Farfado da Tashar Lantarki a Katsina
- Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da shirin farfado da injin samar da wutar lantarki mai karfin 10MW a Lambar Rimi bayan kusan shekaru 20 da daina aiki
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gana da kamfanin Vergnet Groupe a birnin Faris, domin tsara hanyoyin sake dawo da aikin injin
- An kuma bayyana shirin gina tashar samar da wuta mai amfani da hasken rana mai karfin 10MW domin cike gibin samar da wutar lantarki a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana kudirinta na farfado da injin samar da wutar lantarki na Lambar Rimi mai karfin 10MW wanda ya dade ba ya aiki.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da kamfanin Vergnet Groupe, wadanda suka kera kayan aikin tashar a birnin Faris.
Mai magana da yawun gwamna Radda, Ibrahim Kaula Mohammed ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Radda zai farfado da injin lantarkin Rimi
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnati ta dukufa wajen farfado da injin samar da wuta na Lambar Rimi domin inganta lantarki a jihar.
Dikko Radda kara da cewa aikin ya yi daidai da shirin Najeriya na bunkasa makamashi da samar da ingantacciyar wutar lantarki.
Gwamnan ya jaddada cewa aikin zai zama ginshiki ga cigaban jihar Katsina a bangaren samar da wutar lantarki mai dorewa.
Shirin gina wutar sola mai karfin 10MW
A cewar gwamna Radda, gwamnatin jihar za ta kaddamar da wani aikin tashar samar da hasken rana mai karfin 10MW domin cike gibin wutar lantarki a jihar.
Dikko Radda ya ce tashar za ta iya samar da wutar lantarki ga gidaje kusan 4,400 a fadin jihar Katsina.
Katsina za ta zamo cibiyar lantarki
Gwamnan ya bayyana cewa ayyukan da ake shirin kaddamarwa za su taimaka wajen mayar da Katsina cibiyar samar da makamashi a Najeriya
Ya kara da cewa shirin na cikin kokarin jihar Katsina wajen tallafawa Najeriya a matakin kasa wajen samar da lantarki.
An lalata turakan wuta 128 a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin wutar lantarkina TCN ya ce masu lalata kayan gwamnati da yan ta'adda sun lalata turakun wuta har 128.
An samu wannan matsala ne daga watan Janairu a shekarar 2024 zuwa yanzu, wanda ya rika jawo matsalar wuta a jihohin Najeriya.
Asali: Legit.ng