Mafi Karancin Albashi: An Gano Abin da Zai Iya Hana NLC Shiga Yajin Aiki a Disamba

Mafi Karancin Albashi: An Gano Abin da Zai Iya Hana NLC Shiga Yajin Aiki a Disamba

  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta shirya shiga yajin aiki a ranar 1 ga Disamba, amma wasu jihohi sun janye daga wannan shiri
  • Wasu jihohi kamar Imo da Sokoto sun bayyana yarjejeniyar da suka cimma wa da gwamnoninsu kan sabon albashi na N70000
  • Duk da haka, jihohi kamar Kaduna, Nasarawa da Zamfara sun tabbatar da kudurinsu na shiga yajin aiki kamar yadda NLC ta bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwai alamun cewa yajin aikin da kungiyar NLC ta shirya yi a ranar 1 ga Disamba na iya samun cikas, ganin cewa wasu rassan jihohi sun ce ba za su shiga ba.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sabon mafi karancin albashi na N70,000 a watan Yuli, tare da alkawarin duba albashin duk bayan shekaru uku.

Kara karanta wannan

Tinubu ya samu matsala a Arewa, Zulum ya shirya yaƙar dokar sake fasalin haraji

Akwai jihohin da ma'aikata ba za su shiga yajin aiki a Najeriya ba
Ma'aikata a wasu jihohi sun bijirewa NLC na shiga yajin aiki kan sabon albashi. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Jihohin da basu aiwatar da sabon albashi ba

Wasu jihohi, ciki har da Legas da Rivers, sun biya fiye da N70,000, inda suka yi tayin kusan N85,000, abin da ya nuna bambancin matakin bin doka, inji Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, har yanzu akwai jihohi 13 da Abuja da ba su fara aiwatar da sabon lbashin ba, wanda ya bar ma’aikata cikin rashin tabbas kan albashinsu.

Jihohin da ba su fara aiwatarwa ba sun hada da Abia, Akwa Ibom, Ebonyi, Ekiti, Imo, Nasarawa, Kaduna, Katsina, Oyo, Sokoto, Yobe, Zamfara, Enugu da babban birnin Tarayya.

Jihohin da suka janye shiga yajin aiki

Ana shirin yajin aikin, shugaban NLC na Imo, Uche Chigaemezu, ya bayyana cewa ba su da shirin shiga yajin, yana mai cewa sun cimma yarjejeniya da Gwamna Hope Uzodimma.

A Sokoto, amincewar Gwamna Ahmed Aliyu da mafi karancin albashi na N70,000 ta sa NLC ta janye, haka ma shugabannin kwadago a Oyo sun ce ba za su shiga ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin asibiti, sun yi awon gaba da ƙwararren likita a Najeriya

A Katsina, NLC ta tabbatar da janyewa, inda shugaban Hussaini Danduna ya ce sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar, don haka ba su da bukatar shiga yajin aikin.

NLC ta ki amince da hujjojin jihohin

A Akwa Ibom, shugaban TUC, Dominic Abang, ya bayyana cewa ma’aikatan gwamnati ba za su shiga ba, yana mai cewa suna kan tattaunawa a matakin kwamitoci kan sabon albashin.

Duk da janyewar wasu, Kaduna, Nasarawa, Zamfara, da FCT sun tabbatar da shiga yajin aikin, inda shugaban NLC na Kaduna, Ayuba Suleiman, ya tabbatar da hakan.

A gefe guda, ma’ajin NLC na kasa, Akeem Ambali, ya musanta hujjojin jihohin, yana mai cewa jin dadin ma’aikata shi ne babban burin kungiyar, yana kira da a shiga yajin aikin gaba daya.

'Ku hakura da yajin aiki' - Gwamna ga NLC

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Edet Odu, ya buƙaci ƴan ƙwadagon da su haƙura da shiga yajin aikin da suke shirin farawa.

Gwamna Odu ya jaddada kudurinsa na inganta walwalar ma'aikata da waɗanda suka yi ritaya ta hanyar biyan basussukan giratuti, biyan kuɗin fansho a kan lokaci da yin ƙarin girma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.