Gwamna Uba Sani Ya Kori Kwamishina, Ya Nada Wasu Sababbi a Kaduna
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi garambawul a gwamnatinsa yayin da ya naɗa sababbin kwamishinoni
- Malam Uba Sani ya naɗa kwamishinonin kuɗi, tsaron cikin gida da harkokin cikin gida a gwamnatinsa
- Gwamnan ya kuma naɗa manyan masjmu taimaka na musamman kan ɓangarorin daban-daban
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya kori kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan.
Gwamna Uba Sani ya kuma naɗa Dakta James Atung Kanyip a matsayin kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida.

Source: Twitter
Uba Sani ya yi garambawul a gwamnatinsa
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Malam Ibraheem Musa ya fitar, cewar rahoton jaridar The Nation.
Gwamna Uba Sani ya kuma sanar da kafa ma’aikatar jin ƙai, inda aka naɗa Barde Yunana Markus a matsayin kwamishinanta na farko, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
A cewar Gwamnan, naɗin wanda zai fara aiki nan take, na da nufin ƙarfafa tsaro da kuma inganta harkokin mulki a jihar.
"Bugu da ƙari Gwamna Uba Sani ya naɗa Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin kwamishinan kuɗi."
"An kuma naɗa Farida Abubakar Ahmed, a matsayin babbar darakta (Rediyo) a kamfanin yaɗa labarai na jihar Kaduna (KSMC), yayin da Vitus Azuka Ewuzie kasance babban mai taimakawa na musamman kan harkokin shari’a."
- Malam Ibraheem Musa.
Uba Sani ya ba da muƙamai
Sauran muƙaman da aka naɗa sun haɗa da Victor Mathew Bobai a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin jama'a, Abdulmutallib Isah a matsayin babban mataimaki na musamman kan ayyuka na musamman.
Sai Abdulhaleem Ishaq Ringim a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin tattalin arziƙi.
Gwamna Uba Sani ya sake buɗe kasuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya sake bude kasuwar dabbobi ta Kara da ke a Birnin Gwari bayan shekaru 10 tana rufe.
Sake bude kasuwar ya biyo bayan tattaunawa mai tsawo da wakilan kungiyoyin da ba na gwamnati ba, domin kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng
