Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 135, Sun Kubutar da Mutane Masu Yawa
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'adda masu tarin yawa a cikin satin da ya gabata
- Sojojin sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 135 tare da cafke wasu 185 a sassan daban-daban na ƙasar nan
- Jami'an tsaron sun kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su guda 129 a yankuna daban-daban na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 135, a cikin sati ɗaya.
Dakarun sojojin sun kuma cafke mutane 185 da ake zargi, tare da kuɓutar da mutane 129 da aka yi garkuwa da su sassa daban-daban na faɗin ƙasar a cikin satin da ya gabata.
Sojoji sun yi nasara kan ƴan ta'adda
Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manjo Janar Edward Buba ya bayyana hakan ne a hedkwatar tsaro ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
Daraktan yaɗa labaran ya bayyana cewa ƴan ta’adda a yankin Arewa ta tsakiya sun fara miƙa wuya ga sojoji.
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
"A cikin satin da ya gabata, sojoji sun kashe ƴan ta'adda 135 tare da cafke wasu guda 185."
"Sojoji sun kuma cafke mutane 61 da suka aikata laifin satar mai tare da ceto mutane 129 da aka yi garkuwa da su."
"Haka kuma, shugabannin ƴan ta'adda da suka haɗa da kwamandoji da mayaƙa da dama sun miƙa wuya, yayin da wasu masu yawa ke shirin ajiye makamansu."
- Manjo Janar Edward Buba
Sojoji sun yi ƙoƙari
Wani mazaunin jihar Katsina mai suna Kabir Muhammad ya bayyana cewa sojojin sun yi ƙoƙari sosai kan nasarorin da suka samu.
"Wannan abin a yaba ne kuma sun yi ƙoƙari sosai. Muna yi musu fatan Allah ya ci gaba da ba su nasara a yaƙin da suke yi da miyagu."
- Kabir Muhammad
Sojoji sun hallaka ƴan ta'addan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai, sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram.
Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai na CJTF sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan guda biyar a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Jami'an tsaron sun kuma ƙwato makamai a hannun ƴan ta'addan.
Asali: Legit.ng