'Tinubu Zai Yi Rugu Rugu da Tattalin Arzikin Arewa': Bulama Bukarti Ya Fayyace Kudirin Haraji

'Tinubu Zai Yi Rugu Rugu da Tattalin Arzikin Arewa': Bulama Bukarti Ya Fayyace Kudirin Haraji

  • Yayin da ake ta magana kan sabon kudirin haraji da Majalisar Tarayya ta yi zama a kai, Lauya Bulama Bukarti ya magantu
  • Bukarti ya bayyana irin illar da kudirin harajin zai yiwa tattalin arzikin Arewa inda ya ce za a nakasa yankin
  • Lauyan ya koka kan yadda aka yi gaggawar ba kudirin damar tsallake karatu na biyu duk da tasirinsa ga yankin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fitaccen lauya, Bulama Bukarti ya yi magana kan sabon kudirin haraji da ake ta ce-ce-ku-ce a kai.

Bukarti ya ce kudirin da Bola Tinubu ya kawo zai yi rugu-rugu da tattalin arzikin Arewacin Najeriya.

Bulama Bukarti ya fayyace illar kudirin haraji ga Arewa
Lauya, Bulama Bukarti ya fadi illar sabon kudirin haraji da Bola Tinubu ya kawo ga Arewa. Hoto: Audu Bulama Bukarti.
Asali: Facebook

Bulama Bukarti ya magantu kan kudirin haraji

Lauyan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

Mai magani ya dirkawa kansa harsashi a ciki yayin gwada maganin bindiga a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukarti ya ce babu gaskiya kan abin da wasu ke cewa kudirin harajin ba zai yiwa tattalin arzikin Arewa illa ba.

Lauyan ya ce tun shekarar 1999 ba a taba yiwa Arewacin Najeriya Illa a tattalin arziki kamar wannan lokaci ba.

'Illolin harajin Tinubu ga Arewa' - Bulama Bukarti

"Idan har gwamnoni da yan Majalisun Arewa suka bari kudirin da Tinubu ya gabatar na kudi ya wuce a yanzu tattalin arzikin Arewacin Najeriya rugu-rugu zai yi."
"Daman tattalin arzikin yankin ya gama lalacewa, daga hawan wannan gwamnati zuwa yanzu mutane da dama sun fada fatara da yunwa da ake hasashen sun kai miliyan 30."
"Wannan kudirin ba maganar talaucin mutane ake yi ba, gwamnatocin jihohi ne za su dawo su talauce na karshe."
"Idan hakan ta tabbata babu wani gwamna a Arewa da zai iya biyan albashi na ma'aikatan gwamnati har gwamnan Kano."

- Bulama Bukarti

Kara karanta wannan

'Ba a fahimci abin ba': Sanata Barau ya yi karin haske kan haraji, ya fayyace komai

Bukarti ya ce dokokin suna da yawa saboda sun kai shafukan fiye da 300 inda ya ce akwai wasu abubuwa masu kyau a ciki.

Sai dai ya ce an dukunkune su yayin da aka fi magana kan wannan kudiri da zai sauya yadda ake rarraba harajin VAT wanda zai illata Arewa.

Sanata Barau ya magantu kan kudirin haraji

A baya, kun ji cewa ana ta ce-ce-ku-ce kan kudirin haraji da Majalisar Tarayya ta yi zama a kai, Sanata Barau Jibrin ya yi karin haske.

Mataimakin shugaban Majalisar ya fayyace yadda lamarin kudirin haraji ya ke inda ya ce ba a yi komai ba yanzu ma aka fara muhawara a kai.

Hakan ya biyo bayan caccakar sanatocin Arewa da ake yi musamman shi Barau da ya jagoranci zamanta a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.