'Ba a Fahimci Abin ba': Sanata Barau Ya Yi Karin Haske kan Haraji, Ya Fayyace Komai

'Ba a Fahimci Abin ba': Sanata Barau Ya Yi Karin Haske kan Haraji, Ya Fayyace Komai

  • Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan kudirin haraji da Majalisar Tarayya ta yi zama a kai, Sanata Barau Jibrin ya yi karin haske
  • Mataimakin shugaban Majalisar ya fayyace yadda lamarin dokar haraji ta ke inda ya ce ba a yi komai ba yanzu ma aka fara muhawara a kai
  • Hakan ya biyo bayan caccakar sanatocin Arewa da ake yi musamman shi Barau da ya jagoranci zamanta a ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana kan kudirin haraji.

Sanata Barau ya koka kan yadda wasu ke ta zage-zage da sharri kan abin da ba su gama fahimtarsa ba.

Barau Jibrin ya yi ƙarin haske kan sabon kudirin haraji
Sanata Barau Jibrin ya koka kan ce-ce-ku-ce game da kudirin haraji. Hoto: Barau I Jibrin.
Asali: Twitter

Haraji: Sanata Barau ya wayar da kan al'umma

Barau ya bayyana haka a yau Asabar 30 ga watan Nuwambar 2024 cikin wata murya da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Sanata Ali Ndume ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin muryar, an jiyo Barau na wayar da kan al'umma kan abin da ake nufi da kudiri ya tsallake karatu na biyu.

Sanata Barau ya ce tsallake karatu na biyu da kudirin ya yi ba shi ne an gama ba inda ya ce yanzu ma aka fara zama a kai.

'Abin da muka yi kan kudirin haraji' - Barau

"Abin da muka fara yi shi ne neman masana da su zo su yi mana bayani saboda wasu da yawa ba su san abin da ke cikin kudirin ba."
"Sai muka ce a yi zaman Majalisar ranar da kowa ke ganinmu a talabijin a ranar Laraba sai aka kira wasu inda wasu daga cikin Sanatoci suka ce ba su san da zaman ba."
"Ai karatu na biyu kawai wuri ne da mai son magana zai yi magana saboda tsarin dokar haraji sai wanda ya ke da ilimi saboda su duba su zo su fada mana abin da ke ciki."

Kara karanta wannan

'Ya fi bala'in cire tallafi': Sheikh Abubakar Zaria ya yi tofin Allah tsine kan kudurin haraji

- Barau Jibrin

Shehin malami ya soki Barau kan haraji

Kun ji cewa yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan sabon kudirin haraji, Sheikh Abubakar Salihu Zaria ya nuna damuwa kan halin da ake ciki.

Shehin malamin ya kira sunan wasu 'yan siyasa inda ya yi musu addu'o'in bala'i yayin da ya yabawa Sanata Ali Ndume.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.