Wani Jirgi Ɗauke da Mutane Sama da 200 Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Neja
- Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji sama da 200 ya nutse a yankin Dambo-Ebushi a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya
- Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jirgin ya ɗauko mata da masu aikin gona kuma ya kife ne a hanyar zuwa kasuwar Katcha ta mako mako
- Zuwa yanzu masu aikin ceto sun tsamo gawarwakin mutum takwas yayin da ake ci gaba da laluben ragowar fasinjojin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Wani jirgin ruwa da ya ɗauko ɗaruruwan fasinjoji ya kife a yankin Dambo-Ebuchi da ke kogin Niger a jihar Neja yau Juma'a, 29 ga watan Nuwamba.
Ana fargabar mutane da dama sun mutu sakamakon wannan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya afku a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya.
Jirgin ruwan ya ɗauko akalla mutum 200
Ganau sun bayyana cewa jirgin mallakin wani mutumi mai suna, Musa Dangana, ya ɗauko mutane sama da 200 lokacin da ya kife, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun kara da cewa fasinjojin da kwale-kwalen ya ɗauko sun kunshi mata ƴan zuwa cin kasuwa da manoma kuma ya kife ne a hanyar zuwa kasuwar Katcha ta mako-mako.
An ruwaito cewa jirgin ya nutse da dukkan mutanen da ya ɗauko, ana farbagar da yawa daga cikin sun rasu.
Mutum 8 sun mutu a hatsarin jirgin
Tuni dai jami'an kai agajin gaggawa da mutanen da suka iya ruwa suka fara aikin ceto domin tsamo gawarwakin waɗanda suka rasu da ma waɗanda suka tsira.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, an yi nasarar ciro gawar mutum takwas yayin da masu kai agaji na ci gaba da laluben sauran fasinjojin.
Wannan mummunan hatsari na zuwa ne watanni bayan wani makamancin haka ya faru a kogin Muwo Gbajibo da ke karamar hukumar Mokwa ta Jihar Neja a ranar 1 ga Oktoba, 2024.
Jiragen ruwa 2 sun yi hatsari a Delta
Kuna da labarin wasu jiragen ruwa biyu sun yi karo a yankin ƙaramar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta, mutum biyar sun rasa rayukansu.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce wasu sun samu raunuka kuma an kwantar da su a asibiti domin yi masu magani.
Asali: Legit.ng