Jami'in NNPCL Ya Fadawa Yan Najeriya Gaskiya kan Fara Aikin Matatar Fatakwal

Jami'in NNPCL Ya Fadawa Yan Najeriya Gaskiya kan Fara Aikin Matatar Fatakwal

  • Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya fitar da sanarwa kan zargin cewa matatar man gwamnati ta Fatakwal ba ta fara aiki ba
  • Wani mazaunin jihar Rivers, Timothy Mgbere ne ya fito duniya ya ce NNPCL ya boye gaskiya ga yan Najeriya kan fara tace mai a matatar
  • Jami'in yada labaran kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye ya ce ba ƙamshin gaskiya a cikin zargin da Timothy Mgbere ya yi kan matatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya yi martani kan zargin cewa matatar Fatakwal ba ta fara aiki ba.

Wani dan jihar Rivers da ke ikirarin zama a yankin da matatar Fatakwal ke aiki ne ya fito ƙarara ya ya zargi NNPCL da boye gaskiya.

Matatar Fatakwal
NNPCL ya karyata zargin boye gaskiya game da matatar Fatakwal. Hoto: NNPC Limited
Asali: Twitter

Kamfanin NNPCL ya wallafa a Facebook cewa maganganun da Timothy Mgbere ya yi ya nuna bai ma san yadda matatar ke aiki ba balle ya fadi halin da ta ke ciki.

Kara karanta wannan

'Tsohon mai aka saka a matatar Fatakwal,' An zargi NNPCL da rufa rufa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu so masa martani ba saboda ba shi da hurumin yin magana a kan matatar kasancewar shi ba ma'aikaci ba ne, amma hakan ya zama dole saboda kar ya ruɗi yan Najeriya.
Muna tabbatar da cewa bayan samar da man dizil da kalanzir, matatar Fatakwal tana iya tace man fetur lita miliyan 1.4.
Muna kira ga yan Najeriya da su yi watsi da maganganun Timothy Mgbere domin babu gaskiya a cikinsu."

- Olufemi Soneye

Jaridar Punch ta wallafa cewa kamfanin NNPCL ya ce Timothy Mgbere ya ƙaryata kansa da kansa a cikin maganganun da ya yi saboda rashin sanin yadda matatar ke aiki.

NNPCL zai sayar man matatar Fatakwal?

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi ƙarin haske kan fetur da aka fara samarwa a matatar Port Harcourt a Rivers.

Babban jami'in sadarwa na NNPCL ya bayyana cewa za a riƙa sayar da fetur ɗin ne kawai ga gidajen man kamfanin NNPCL.

An ruwaito cewa Olufemi Soneye ya nuna ba a fara sayar da fetur ɗin da yawa ba kuma ba a buɗe wajen sayarwa ba a halin yanzu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng