'Ba Zai Shafi Talaka ba': An Gano Dalilin Tinubu na Gabatar da Dokar Gyaran Haraji
- Gwamnatin tarayya ta ce dokar gyaran haraji za ta inganta tsarin tattalin arziki, kuma za a mayar da hankali kan harajin kamfanoni
- Mai Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa, Sunday Dare ya ce dokar za ta saukaka haraji ga talaka da kananan 'yan kasuwa
- Sunday Dare ya ce tsarin zai ba jihohi damar ƙara kudin shiga ta hanyar jawo masu saka jari da haɓaka harajin VAT daga yankunansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mai ba shugaba Bola Tinubu shawara, Sunday Dare, ya ce an gabatar da dokokin gyaran haraji domin samar da tsarin haraji mai nagarta.
Sunday Dare, tsohon ministan wasanni a karkashin gwamnatin Buhari, ya bayyana cewa sama da kashi 80% na harajin yanzu ba sa amfanar Najeriya.
A ziyarar da ya kai ofishin jaridar Premium Times, Dare ya ce wannan gyaran zai ba da karfi ga karbar harajin kamfanoni domin samun kudaden shiga masu dorewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin shugaban kasar ya ce an fara amfani da wannan tsarin a Lagos tsakanin 1999 zuwa 2007, lokacin da Tinubu ke gwamna, kuma tsarin ya kawo ci gaba sosai.
Kalubalen gwamnoni da muhawara a majalisa
Dokokin gyaran haraji da ke gaban majalisar dattawa sun haifar da muhawara mai zafi tsakanin 'yan majalisa da kuma jama'ar kasar.
Watanni biyu da suka gabata, Tinubu ya gabatar da dokoki hudu, ciki har da na VAT, wanda gwamnoni daga Arewa suka ce zai cutar da yankin.
Kungiyar Gwamnonin Arewa ta umarci 'yan majalisar su kauracewa dokokin saboda illar da suke tunanin zai yi ga ci gaban shiyyar.
Duk da wannan adawar, Tinubu ya nace cewa a warware duk wani sabani ta hanyar muhawara a majalisa maimakon ace a janye dokokin.
Hadimin Tinubu ya magance damuwar jama'a
Sunday Dare ya bayyana cewa gyaran harajin zai rage nauyin haraji ga masu ƙaramin ƙarfi da ƙananan 'yan kasuwa kuma ba zai shafi talaka ba.
A ƙarƙashin tsarin, ba za a karbi haraji kan wadanda ke samun ƙasa da Naira miliyan ɗaya a shekara da kamfanonin da ke samun ribar ƙasa da Naira miliyan 50 ba.
Ya jaddada cewa gyaran zai inganta tsarin tattalin arziki na tarayya, inda jihohi za su jawo masu saka jari da ƙara kudaden harajin VAT.
Hadimin shugaban kasar ya ce Tinubu ba ya son haraji ya shafi talakawa, sai dai ya tabbata tsarin zai habaka arziki domin kawo ci gaba mai dorewa.
Zulum ya ki amincewa da dokar haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya soki dokar gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa Majalisa.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa dokar ba ta da amfani ga jihohin Arewa da wasu jihohin Kudu, yana nanata matsayarsa na adawa da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng