Sauya Suna: NYSC Ta Gyara Dokar Matan Aure da Musulmi Suka Daɗe Suna Nema

Sauya Suna: NYSC Ta Gyara Dokar Matan Aure da Musulmi Suka Daɗe Suna Nema

  • Hukumar mai lura da matasa ma su yi wa kasa hidima ta NYSC ta yi kwaskwarima ga wasu dokokinta da suka shafi matan aure
  • A sabuwar dokar, an cire sharadin saka sunan miji ga matan aure kafin a tura su hidima yankunan da mazajesu ke zama ko aiki
  • A dalilin haka, hukumar NYSC ta bukaci dukkan shugabanninta a jihohi 36 da FCT Abuja su tabbatar da sabon sauyin da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar NYSC ta cire sharadin sauya suna ga matan aure kafin a tura su wurare hidima.

Rahotanni na nuni da cewa darakta mai lura tura matasa wuraren hidima, Abubakar Muhammad ne ya sanar da hakan.

NYSC matan aure
NYSC ta soke dokar amfani da sunan miji ga matan aure. Hoto: National Youth Service Corps
Asali: Twitter

Rahoton Jaridar Punch ya tabbatar da cewa a ranar 25 ga watan Nuwamba hukumar NYSC ta fitar da sanarwar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe dattijo mai shekaru 85 bayan karɓar kudin fansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cire amfani da sunan miji a NYSC

Hukumar NYSC ta sanar da cewa an cire sharadin amfani da sunan miji ga matan aure a lokacin yin rajista.

Dama al'ummar Musulmi sun dade suna bukatar hakan kasancewar addini bai aminta da mace ta yi amfani da sunan miji ba, sai sunan mahaifi.

Daily Post ta wallafa cewa darakta mai lura da tura masu hidimar kasa wurare, Abubakar Muhammad ne ya tabbatar da soke dokar a Abuja.

"Hukumar NYSC ta amince da sauya dokar da ta tilastawa matan aure amfani da sunan miji kafin a tura su wuraren hidima.
Saboda haka, shugabannin NYSC a jihohi su san da cewa daga yanzu ba sai matan aure sun yi amfani da sunan miji ba.
Sai dai kuma dukkan sauran sharudan da suka shafi matan aure suna nan kamar yadda aka sani."

- Abubakar Muhammad

Bayan sauya dokar, NYSC ta buƙaci shugabanni da su tabbatar da an yi aiki da sabon hukuncin yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

"Mun Haramta Hayaniya," Gwamnatin Legas ta rufe babban wurin ibada da wasu otel

'Yan NYSC sun bukaci fara biyan N77,000

A wani rahoton, kun ji cewa masu yi wa ƙasa hidima da aka fi sani da ƴan NYSC sun koka kan rashin aiwatar da sabon alawus da gwamnati ta yi alƙawari.

Matasan sun roki gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta ɗauka saboda a halin da ake ciki N33,000 ba ta ɗaukar dawainiyarsu a wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng