Badakalar N110bn: EFCC Ta Gaza Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kogi a Kotu

Badakalar N110bn: EFCC Ta Gaza Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kogi a Kotu

  • Hukumar EFCC ta gaza gurfanar da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello a kotu a ranar 28 ga Nuwamba, 2024, saboda wasu dalilai
  • Yahaya Bello na fuskantar tuhume-tuhume 19 na zambar N82bn, bayan an tsare shi a wata tuhumar zambar N110.4bn da ake masa
  • Kotu ta dage sauraron shari'ar zuwa shekarar 2025, domin yanke hukunci kan gurfanarwar da duba kuma hukuncin Kotun Koli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shari'ar badakalar N110.4bn da EFCC ke yi da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ta samu tsaiko a ranar Alhamis, 28 ga Nuwamba.

Hakan ya faru ne bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta gaza gabatar da Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Hukumar EFCC ta gaza gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu
Rashin wasu takardu ya sa hukumar EFCC ta gaza gurfanar da Yahaya Bello a kotu@OfficialGYBKogi, @officialEFCC
Asali: Twitter

EFCC ba ta gurfanar da Yahaya Bello ba

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito da kotu ta garkame yan sanda 2 da jami'in hukumar NIS a Gombe

Tun da farko an shirya sake gurfanar da Bello a kan tuhume-tuhume 19 na zambar kudi da suka kai Naira biliyan 82, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gurfanar da tsohon gwamnan ya biyo bayan tsare shi da wata babbar kotun Abuja ta yi bisa tuhume-tuhume 16 na zambar Naira biliyan 110.4.

Amma majiyoyi a kotun sun bayyana cewa rashin kammala takardun da ake bukata ne ya hana kotun saka batun a cikin jerin shari’unsu na ranar.

An sanya ranar sake shiga kotu

Haka kuma, Mai Shari’a Emeka Nwite ya dage sauraron shari'ar zuwa 21 ga Janairu, 2025, don yanke hukunci kan gurfanarwar da kuma sakamakon ƙarar da ke gaban Kotun Koli.

Sakamakon haka, lauyoyin EFCC da jami’an tsaro da suka riga sun mamaye harabar kotun sun kama gabansu da misalin karfe 12 na rana, a cewar rahoton.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 18, gwamnatin tarayya ta sanya ranar gudanar da ƙidaya a Najeriya

Shari’ar ta fuskanci jinkiri da dama sakamakon rashin bayyanar tsohon gwamnan a gaban kotun, sai dai yanzu ana ganin za a iya ci gaba tunda ya na tsare.

Yahaya Bello ya musanta tuhumar EFCC

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya shaidawa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa tuhumar da EFCC ke yi masa ba gaskiya ba ce.

Yahaya Bello ya jaddadawa kotun cewa bai aikata ko daya daga cikin tuhume tuhume 16 da hukumar yaki da cin hancin da rashawar take yi masa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.