"Akwai Lauje cikin Nadi": Sanata Ndume Ya Fadi Abin da Ya Hango a Dokar Haraji

"Akwai Lauje cikin Nadi": Sanata Ndume Ya Fadi Abin da Ya Hango a Dokar Haraji

  • Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya nuna shakku kan ƙudirin dokar sake fasalin haraji da aka bijiro da shi
  • Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa akwai alamun tambaya kan yadda takwarorinsa suka yi gaggawar amincewa da ƙudirin
  • Ndume ya bayyana cewa akwai matsaloli da za a fuskanta idan gwamnoni musamman na Arewa ba su goyi bayan ƙudirin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya nuna damuwa kan kuɗirin dokar sake fasalin haraji.

Sanata Ndume ya nuna damuwarsa kan yadda takwarorinsa a majalisar dattawa suka amince da dokar sake fasalin haraji. 

Ndume ya magantu kan dokar haraji
Sanata Ndume ya nuna shakku kan kudirin dokar haraji Hoto: Sen. Mohammed Ali Ndume
Asali: Twitter

Ali Ndume ya nuna shakku kan dokar haraji

Sanata Ndume ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Sanata Ali Ndume ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume ya nuna shakku kan gaggawar sake fasalin haraji, inda ya yi nuni da cewa an ɗauki shekaru 10, a majalisa kafin ta zartar da ƙudirin dokar masana'antar man fetur (PIB).

Ya bayyana cewa akwai alamar tambaya kan yadda aka yi saurin amincewa da ƙudirin, musamman game da rawar da ɓangaren zartaswa ya taka.

A ranar Alhamis ne dai ƙudirin dokar sake fasalin harajin, ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa.

Wace shawara Sanata Ndume ya ba da?

Yayin da Ndume ya bayyana cewa ba ya adawa da ƙudirin kuma yana goyon bayan nasarar shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya buƙaci a janye shi domin ci gaba da tattaunawa a kansa.

Ya kuma yi gargaɗin cewa idan gwamnonin jihohi musamman na Arewa ba su goyi bayan ƙudirin ba, hakan zai iya haifar da wasu matsaloli.

Ndume ya magantu kan dokar haraji

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya bayyana dalilansa na kin goyon bayan kudurin haraji wanda gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta tafka muhawara, kudirin harajin Tinubu ya tsallake karatu na 2

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa lokacin da gwamnatin Najeriya ta zaba na kawo dokar harajin, ko kaɗan bai dace ba.

Ya nuna cewa Najeriya ƙasa ce da ke fama da matsaloli da yawa, daga cikinsu akwai yunwa da rashin abin hannu a wajen jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng