Bayan Shekaru 10 Tana Rufe, Gwamna Ya Bude Babbar Kasuwar Dabbobi a Kaduna
- Gwamna Uba Sani ya sake bude kasuwar dabbobi ta Kara a Birnin Gwari, bayan shafe shekaru 10 tana rufe saboda matsalar tsaro
- Tattaunawa tsakanin gwamnati da shugabannin ’yan bindiga ta kai ga yarjejeniyar zaman lafiya da kawo karshen rikicin yankin
- Gwamnan jihar Kaduna ya ce ana shirin dawo da wutar lantarki da sadarwa, tare da tabbatar da zaman lafiya a Birnin Gwari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - An cika da murna a Kaduna yayin da Gwamna Uba Sani ya sake bude kasuwar dabbobi ta Kara da ke a Birnin Gwari bayan shekaru 10 tana rufe.
Sake bude kasuwar ya biyo bayan tattaunawa mai tsawo da wakilan kungiyoyin da ba na gwamnati ba, domin kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
Uba Sani ya sake bude kasuwar dabbobi
Gwamna Uba Sani ya sanar da sake bude kasuwar ta Kara a shafinsa na X a daren ranar Alhamis, 28 ga Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar gwamnan jihar na Kaduna ta ce:
"An yi murna da farin ciki a Birnin Gwari yayin da na sake bude shahararriyar kasuwar dabbobi ta Kara, wanda ke nuni da dawowar harkokin kasuwanci da zaman lafiya a yankin.
"Kungiyar Tattaunawar Zaman Lafiya da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa tare da hadin gwiwar hukumomin tarayya da na tsaro suka jagoranci yarjejeniyar zaman lafiyar."
Shugabannin 'yan bindiga sun ajiye makamai
Gwamna Uba Sani ya ce wasu shugabannin 'yan bindiga da mabiyansu sun mika makamansu, "inda suka rungumi zaman lafiya don kawo karshen rikicin".
"An sanya wadannan mutanen da suka tuba cikin shirin gyaran hali da gwamnatin jihar Kaduna ta assasa tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya."
"Bangarorin biyu sun yi alkawarin bin ka'idojin yarjejeniyar zaman lafiyar, kuma gwamnati za ta yi amfani da tsarin a wuraren da ke fama da rikici."
- A cewar Gwamna Uba Sani.
Za a dawo da wuta a Birnin Gwari
Sanarwar ta ce ana shirye-shiryen dawo da wutar lantarki da sadarwa a Birnin Gwari, wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da habaka tattalin arziki.
Gwamna Uba Sani ya jaddada aniyarsa na kula da zaman lafiya a Birnin Gwari, yana mai fatan cewa za a samu zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar.
Asali: Legit.ng