'An Kashe Mutum 24, An Cafke 1,200': Amnesty Ta Saki Rahoton Zanga Zangar Agusta

'An Kashe Mutum 24, An Cafke 1,200': Amnesty Ta Saki Rahoton Zanga Zangar Agusta

  • Amnesty International ta ce an kashe mutane 24 yayin zanga-zangar #EndBadGovernance daga 1 zuwa 10 ga Agusta a Najeriya
  • Rahoton ya nuna an kama mutane 1,200 yayin zanga-zangar, tare da yi musu azaba da cin zarafi, ciki har da yara da matasa
  • Amnesty ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gudanar da bincike kan take hakkin bil’adama, tare da bin kadin wadanda aka zalunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarid

Amnesty International ta ce akalla masu zanga-zanga 24 ne aka kashe yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a Najeriya.

'Yan Najeriya sun gudanar da zanga-zangar gama gari na tsawon kwanaki 10 daga 1 ga Agusta, suna adawa da matsalolin rayuwa da suka yi kamari.

Amnesty ta fitar da rahoton zanga zangar Agusta
Amnesty ta aika sako ga Tinubu yayin da ta fitar da rahoton zanga zangar Agusta. Hoto: amnesty.org
Asali: UGC

The Cable ta ce zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a wasu sassan kasar, inda ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga da ‘yan jarida.

Kara karanta wannan

Ban da zanga zanga: Osinbajo ya fadi hanya 1 da matasa za su kawo canji a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan sanda sun yi amfani da karfi" - Amnesty

An samu rahotannin satar kaya da lalata dukiyoyin gwamnati da na jama’a a wasu jihohin Arewa musamman Kano, Kaduna, Jigawa da sauransu.

A cikin sabon rahoton da Amnesty International ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an kama masu zanga-zanga kusan 1,200 yayin wannan gagarumar zanga-zanga.

Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta ce hukumomin Najeriya "sun yi ukuba da sauran munanan cin zarafi kan masu zanga-zanga.”

Ta kuma kara da cewa murkushe masu zanga-zangar “ya nuna gazawar hukumomin Najeriya wajen mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki.”

"An kashe mutane 24, an kama 1,200" - Amnesty

Rahoton ya bayyana cewa:

“Amnesty International ta gano cewa hukumomin Najeriya sun kashe akalla masu zanga-zanga 24 tare da kama 1,200 yayin zanga-zangar #EndBadGovernance tsakanin 1 zuwa 10 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu Bayan Tinubu Ya Kore Ta

“Adadin wadanda suka mutu na iya wuce 24 saboda kokarin hukumomi na boye wannan aika-aika."

A yayin gabatar da rahoton a Kano, Isa Sanusi, daraktan Amnesty International a Najeriya, ya ce yara biyu da matasa 20 ne aka kashe yayin zanga-zangar.

Sanusi ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun shaida “matakin rashin doka mai tsanani” inda ‘yan sanda suka harba harsasai kai tsaye kan masu zanga-zanga.

Amnesty ta bukaci Tinubu ya yi bincike

Ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya binciki zargin take hakkin bil’adama tare da tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa sun samu diyya.

“Mutane biyu sun ji rauni bayan harbin ‘yan sanda a hannu da kafafu, wasu kuma sun galabaita saboda hayaki mai sa hawaye.
"Yin zanga-zanga cikin lumana kan manufofin gwamnati ya zama batun rai da mutuwa a Najeriya.
“Dole Shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa su gudanar da bincike cikin gaggawa, tsanaki, da gaskiya kan take-taken hakkin bil’adama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance."

Kara karanta wannan

'Ban saka shi ba': Gwamna ya fusata da katobarar hadiminsa, ya dakatar da shi

- A cewar Sanusi.

Zanga zanga: 'Yan sanda sun budewa wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a lokacin da suka yi yunkurin toshe babban titi a Minna, babban birnin jihar Neja.

An dai jiyo karar harbe-harben bindiga da matasan suka matsa sai sun toshe titin bayan sun fara zanga-zanga a ranar Alhamis, 1 ga Agustar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.