'Yan Bindigan da Suka Sace Yara a Kaduna Sun Fadi Kudin Fansan da Suke So
- Ƴan bindigan da suka sace wasu yara a Kaduna sun tuntuɓi mahaifinsu domin ya ba su kuɗin fansa kafin su sake shaƙar iskar ƴanci
- Hatsabiban ƴan bindigan sun buƙaci a ba su N300m a matsayin kuɗin fansa kafin su saki yaran waɗanda suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Chikun
- Mahaifin yaran ya nuna damuwar cewa ƴan bindigan sun fara yin barazanar kashe yaran idan ba a kai musu kuɗaɗen ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa, Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƴan bindigan da suka sace wasu yara a Kaduna sun bayyana kuɗin fansan da za a ba su.
Masu garkuwa da mutanen sun kira mahaifin yaran da suka sace inda suka buƙaci a ba su N300m, kafin su saki yaran.
Ƴan bindiga sun yi barazana
Daily Trust ta rahoto cewa masu garkuwa da mutanen sun yi barazanar kashe ɗan ƙarami daga cikin yaran saboda kukan da yake yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun kuma shaidawa mahaifin yaran mai suna Adamu, cewa ko dai ya biya kuɗin fansan ko kuma su kashe su.
Adamu, wanda yake zaune a Keke A, ƙaramar hukumar Chikun, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun yi wa yaran duka saboda ya roƙe su kan kuɗin fansan da suka buƙata.
"Sun kira ni, sun buƙaci a ba su N300m, lokacin da na roƙe su, ina ji suna dukan yaran. Ina buƙatar addu'a."
- Adamu
An dai sace yaran ne bayan mahaifinsu ya fita gida a daren ranar Talata domin zuwa wajen mahaifiyarsu da ke kula da tagwayensu da aka kwantar a asibiti.
Ƴan bindiga sun kashe wani dattijo
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace wani dattijo mai shekaru 85, mai suna Deh Idi Dakum a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Matelem a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka dattijon bayan sun karɓi kuɗin fansa daga hannun iyalansa.
Asali: Legit.ng