Basarake Ya Dakatar da Nadin Sarki da Ake Yi, Ya Haramta ba da Sarauta Ta bayan Fage
- Olubadan na jihar Oyo, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya dakatar da nadin sarauta da aka shirya yi a yau Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024
- Basaraken ya ba da umarnin hana duk wani shirin nadin sarauta ba tare da sahalewarsa ba a fadin jihar baki daya
- Wannan na zuwa ne yayin da wasu kungiyoyi suka shirya nada Iyalode na Oyo a yau Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Fitaccen basarake a jihar Oyo ya dakatar da nadin sarauta da aka shirya yi ba bisa ka'ida ba.
Sarkin Ibadan da ake kira Olubadan, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya dauki matakin ne saboda an saba doka.
Oyo: Basarake ya dakatar da nadin sarauta
Tribune ta ce kwamitin masarautar ya dakatar da nadin Iyalode na Oyo da wasu gungun mutane suka shirya yi ba bisa ka'ida ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin ganawar kwamitin da ya samu halartar sarakunan gargajiya daban-daban, kwamitin ya umarci dakatar da duka wata nadin sarauta.
Kwamitin ya yi magana musamman kan nadin sarautar da aka shirya yi a yau Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024.
Olubadan ya ba da umarni kan nadin sarauta
Har ila yau, kwamitin ya nuna damuwa kan yadda ake nadin sarauta babu ka'ida da kuma bin tsarin da ya saba dokar masarautu musamman tsakanin yan kasuwa.
Olubadan ya ce nadin sarauta da ta samu amincewar masarautar ce kawai halattacciya a fadin jihar, cewar Vanguard.
Daga bisani kwamitin masarautar ya bukaci yan kasuwa maza da mata da su mayar da hankali kan siye da siyarwa madadin fafutukar neman matsayi na sarauta ko siyasa.
Abba Kabir ya roki alfarmar sarakunan gargajiya
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana muhimmancin sarakunan gargajiya game da tsare-tsaren gwmantinsa.
Gwamnan ya bukaci goyon baya daga sarakunan gargajiya duba da yadda suke kusa da al'umma wurin wayar musu da kai.
Hakan na zuwa ne yayin da hadimin gwamnan a bangaren masarautu ya kai ziyara ta musamman a fadar Sarkin Rano.
Asali: Legit.ng