Hafsan Sojojin Kasa Ya San Matsayinsa bayan Tantance Shi a Majalisa

Hafsan Sojojin Kasa Ya San Matsayinsa bayan Tantance Shi a Majalisa

  • Majalisar wakilai ta kammala aikin tantance babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede
  • Kwamitin da aka ɗorawa alhakin tantance Olufemi Oluyede ga gabatar da rahotonsa inda ya bayyana gamsuwa da halayensa, ƙwarewarsa da gogewarsa
  • Daga ƙarshe majalisar ta tabbatar da naɗin da aka yi wa Oluyede a matsayin babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa, Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta tabbatar da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya (COAS).

Tabbatar da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojojin ƙasan na zuwa ne bayan an tantance shi a ranar Laraba.

Majalisar wakilai ta tabbatar da Olufemi Oluyede
Majalisar wakilai ta tabbatar da Olufemi Oluyede a matsayin hafsan sojojin kasa Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Kwamiti ya tantance hafsan sojojin ƙasa

Jaridar The Cable ta rahoto cewa an tabbatar da Oluyede ne bayan an miƙa rahoto kan tantancewar da aka yi masa.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 135, sun kubutar da mutane masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar wakilan ta tabbatar da Olufemi Oluyede ne bayan gabatar da rahoton Babajimi Benson, shugaban kwamitin tsaro, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai kan sojoji da tsaro ya tantance Olufemi Oluyede a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamban 2024.

An gamsu da halayen Janar Oluyede

Yayin da yake gabatar da ƙudirin neman a duba rahoton, Babajimi Benson ya bayyana cewa an yi wa Oluyede tambayoyi kan dangantaka tsakanin hukumomin tsaro da sauran abubuwan da suka shafi sojoji.

Ya bayyana cewa Oluyode ya gabatar da kansa yadda ya dace kuma kwamitin ya gamsu da karatunsa, gogewarsa, ƙwarewarsa, halayyarsa da ɗabi'unsa.

Daga nan sai majalisar ta karɓi rahoton tare da tabbatar da naɗin Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojojin ƙasa.

Hafsan tsaro ya koka kan masu ba sojoji cikas

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana masu kawo cikas wajen shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Kungiya ta karrama Matawalle, ta fadi nasarorin da ya samu a Minista

Babban hafsan hafsoshin ya bayyana cewa masu kai wa ƴan ta'adda ababen fashewa da masu ba da bayanai, su ne manyan masu kawo matsala a yaƙin da ake yi da ta'addanci a wasu sassan ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng