Bulama Ya Maimata Kalaman Hamdiyya, Ya Kalubalanci Gwamnatin Sakkwato Ta Kama Shi
- Barista Bulama Bukarti ya soki gwamnatin Ahmed Aliyu a jihar Sakkwato a kan cin zarafin Hamdiyya Sidi Shareef
- Mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya ce babu wani kuskure ko laifi a cikin kalamanta na neman a tabbatar da tsaro
- Bulama ya yi mamakin yadda gwamnan ke ganin mai dakinsa da yaransa da ke gidan gwamnati sun fi na jama'a daraja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta ko ware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Dan gwagwarmaya kuma mai fafutukar kare hakkin 'dan Adam, Barista Bulama Bukarti ya soki gwamnati bayan an ci zarafin matashiya Hamdiyya Sidi Shareef.
Hamdiyya ta fada mummunar matsala bayan ta roki gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu ya kawo karshen cin zarafin mata da 'yan bindiga ke yi.
A hirarsu ta cikin shirin Fashin Baki, Dr. Bulama Bukarti ya yi mamakin yadda gwamnan ya dauki kalaman Hamdiyya a matsayin barazana ko rashin da'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bulama Bukarti ya caccaki gwamnan Sakkwato
Wani mai amfani da shafin X, Taller ya wallafa bidiyon Bulama Bukarti ya na cewa babu kuskure a kalaman Hamdiyya.
Bulama Bukarti ya kara da cewa;
"Maganar dai ita ce baiwar Allah nan ta na sukar gwamnatin Sakkwato a kan maganar rashin tsaro."
Bulama ya kalubalanci gwamnatin jihar Sakkwato
Barista Bukarti ya yi mamakin yadda aka yi har wasu da ake zargin mukarraban gwamnatin Sakkwato ne su ka ci zarafinta har da barazanar kisa.
Ya ce;
"Kuma ni ma na fada, gwamnan Sakkwato, in ya so ka sa a kama ni, ka kwatanta, in gidanka aka tsallaka, aka yi lalata da matarka, haka za ka yi?"
"Abin da aka yi mutanen Sakkwato, in 'ya'yanka na cikinka aka yi wa abin da aka yi wa 'ya'yan Sabon Birni, haka za ka yi?"
Ya koka bisa yadda gwamna Ahmed Aliyu ke ganin iyalansa sun fi sauran mutanen Sakkwato da 'yan bindiga ke cin zarafinsu babu kakkautawa.
Bulama Bukarti ya shawarci gwamnati
A baya, kun ji cewa mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Bulama Bukarti ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta dage wajen fattakar miyagun Lakurawa kafin su kara kwari.
Ya bayyana cewa akwai bayanan da ke nuni da yadda 'yan kungiyar ta'addancin su ka mamaye wasu sassan jihar Kebbi da Sakkwato, tare da mallakar miyagun makaman yaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng