NNPCL Ya Bayyana Wadanda Matatar Port Harcourt Za Ta Sayarwa Man Fetur
- Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi ƙarin haske kan fetur da aka fara samarwa a matatar Port Harcourt a Rivers
- Babban jami'in sadarwa na NNPCL ya bayyana cewa za a riƙa sayar da fetur ɗin ne kawai ga gidajen man kamfanin NNPCL
- Olufemi Soneye ya nuna ba a fara sayar da fetur ɗin da yawa ba kuma ba a buɗe wajen sayarwa ba a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa, Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya bayyana waɗanda za a riƙa sayarwa da fetur na matatar Port Harcourt.
Babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa fetur da aka samar a matatar ta Port Harcourt, za a sayar ne kawai ga gidajen sayar da man NNPCL.
Matatar Port Harcourt ba ta fara sayar da fetur ba
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Olufemi Soneye ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soneye ya fayyace cewa matatar ba ta fara sayar da fetur ɗin da yawa ba kuma ba ta buɗe wajen da za a riƙa saya ba.
Ya kuma ƙara da cewa kamfanin NNPCL yana ci gaba da sayar da fetur da ya samo daga matatar man Dangote.
Su wanene NNPCL zai sayarwa man fetur?
"Har yanzu ba mu fara sayar da fetur mai yawa ba, kuma har yanzu ba mu buɗe wajen saya ba yayin da muke ci gaba da kammala matakan da suka dace."
"A halin yanzu, fetur da muke sayarwa wanda muka sayo ne daga matatar Dangote."
"A yanzu fetur da aka samar daga matatar Port Harcourt na gidajen man fetur ɗin mu ne. Muna duba farashin mu a kai-a kai tare da daidaita su kamar yadda ake buƙata."
- Olufemi Soneye
Matatar man Port Harcourt ta fara aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers ta fara aikin tace ɗanyen mai bayan tsawon lokaci ba ta aiki.
Babban jami'in sashen sadarwa na kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL, Femi Soneye ne ya tabbatar da hakan ga menama labarai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng