Wasu Gwamnonin Arewa sun bi Tinubu Faransa, an Fadi Abin da za Su Tattauna
- A ranar Laraba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da matarsa suka tafi kasar Faransa bisa gayyata da aka yi wa Najeriya
- Biyo bayan tafiyar shugaban kasar, wasu gwamnonin Najeriya sun taka masa baya domin shiga tattaunawar da za a yi
- Shugaban gwamnonin Arewa ta Yamma, Dikko Umaru Radda na cikin waɗanda suka taka baya ga shugaba Tinubu zuwa Faransa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
France - Wasu gwamnonin Najeriya sun bi shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa Faransa domin tattaunawa ta musamman.
Shugaban gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdularzaq na cikin waɗanda suka bi Bola Tinubu daga Arewa.
Hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya wallafa hotunan gwamnonin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnoni sun bi Tinubu Faransa
Wasu gwamnoni sun bi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Faransa domin tattaunawa da jami'an kasar.
Bayan isar gwamnonin, sun kai ziyarar ban girma ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a masaukinsa na kasar Faris.
A yau Juma'a, 28 ga Nuwamba ne shugabannin kasashen za su tattauna kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar.
"Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya shiga tafiyar shugaba Bola Tinubu ta kasar Faransa.
Sauran fitattun shugabanni sun hada da gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdularzaq, Gwamnan Benue, Hyacinth Aliya".
- Ibrahim Kaulaha Muhammad
Sauran gwamnoni daga Kudancin Najeriya da ke cikin tafiyar sun hada da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu da na jihar Enugu, Peter Mba.
Haka zalika ministan tsaro, Badaru Abubakar ya wallafa a Facebook cewa yana cikin tafiyar shugaban kasar.
A zaman da za su yi, ana kyautata zaton za su tattauna ne a kan yadda za a haɓaka tattalin arziki da kyautata alakar Najeriya da Faransa.
Kashim Shettima ya tafi taro Cote d'Ivoire
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima, ya tafi Cote d'Ivoire domin halartar taron SIREXE na shekarar 2024.
Kashim Shettima zai halarci taron ne domin ya amsa gayyatar da mataimakin shugaban ƙasar Cote d'Ivoire, ya yi masa.
Asali: Legit.ng