TCN Ta Fadi Biliyoyin da Gwamnatin Tinubu Ta Kashe a Gyaran Turakun Wuta 128

TCN Ta Fadi Biliyoyin da Gwamnatin Tinubu Ta Kashe a Gyaran Turakun Wuta 128

  • Kamfanin wutar lantarki ya ce masu lalata kayan gwamnati da yan ta'adda sun lalata turakun wuta har 128
  • An samu wannan matsala ne daga watan Janairu a shekarar 2024 zuwa yanzu, wanda ya rika jawo matsalar wuta
  • Shugaban TCN na kasa, Injiniya Suleiman Ahmed Abdulaziz, ya ce an kashe sama da Naira biliyan takwas wajen gyara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce akalla turakaun wutar lantarki 128 aka lalata a bangarori daban daban na kasar nan.

Shugaban kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN), Injiniya Suleiman Ahmed Abdulaziz, ne ya bayyana haka a wani taro a Abuja.

Mission
An kashe N8.8bn a gyaran turakun lantarki Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Injiniya Suleiman Ahmed Abdulaziz, ya ce sai da gwamanti ta kashe biiyoyin Naira domin gyara turakun domin wadata jama’a da hasken wuta.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara tuhumar Tinubu saboda batun karbo aron Naira Tiriliyan 1.7

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘An kashe N8.8bn a gyara turakun wuta,’ TCN

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na kasa ya ce gwamnatin tarayya ta kashe Naira biliyan 8.8 wajen gyara turakun wuta 128.

Shugaban kamfanin, ya ce daga ranar 13 ga Janairu zuwa yanzu, masu lalata kayan gwamnati da yan bindiga sun lalata turakun wuta sama da 100.

Kamfanin TCN na takaicin lalata turakun wuta

Kamfanin TCN ya bayyana rashin jin dadin yadda jama’a ke cigaba da rufe idanunsu wajen lalata turakun wuta da sauran kayan wutar lantarki.

Injiniya Suleiman Ahmed Abdulaziz, ya ce;

"Abin takaici ne cewa duk lokacin da aka kama masu lalata kayan, kuma an mika su ofishin ‘yan sanda don gurfanarwa sai ‘yan sanda su saka laifin sata a maimakon lalata kayayyakin gwamnati.
"A kan haka ake samun damar bayar da su beli. Idan aka gurfanar da su bisa laifin lalata kayan gwamnati, ba za a ba su beli ba."

Kara karanta wannan

NNPP da APC: Yadda yan siyasa ke wasa da masarautar Kano

"'Yan ta'adda sun lalata turakun wuta," TCN

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Najeriya (TCN), ya tabbatar da cewa an samu wasu 'yan bindiga da su ka kara lalata wasu turakun wuta.

Kamfanin ya ce TCN bata garin sun kai hari kan turken wuta na Ahoada-Yenagoa 132kV tare da sace wasu daga cikin muhimman kayayyakin lantarki, kuma hakan zai kawo cikas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.