Sojoji Za Su Magance Ta'addanci, Dakaru Sun Fadawa 'Yan Arewa Abin da Suke Bukata
- Sojojin kasar nan sun bayyana yadda jama'a za su taka rawa wajen magance matsalar rashin tsaro a Arewa
- Kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Oluyinka Olalekan Soyele ne ya fadi bukatarsu
- Kwamandan ya nemi mazauna Arewa maso Yamma su rika taimaka masu da bayanan sirri kan miyagun mutanen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Oluyinka Olalekan Soyele, ya bayyana daya daga cikin hanyoyin da za a bi don yin nasara a kan 'yan ta’adda.
Kwamandan ya fadi hakan ne a lokacin da ya karbi kungiyar tsofaffin sojoji ta Najeriya watau Nigerian Legion reshen jihar Zamfara, karkashin jagorancin Aminu Ladan Mada.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Manjo Janar Olalekan Soyele ya ce matukar aka karbi tayin da su ka yi, za a samu rangwame sosai na harkokin ta’addanci a Arewa maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta’addanci: Sojoji na neman hadin kan 'Yan Arewa
Kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma ya bukaci jama’a da su ribanya taimakon da su ke ba su wajen yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.
Kwamandan ya bayyana cewa an sake fasalin rundunar zuwa Operation Fansan Yamma na nufin karfafa martanin sojoji kan matsalolin tsaro da su ka addabi mazauna shiyyar.
Shirin sojoji wajen yakar ta’addanci a Arewa
Manjo Janar Oluyinka Olalekan Soyele, ya jaddada cewa sojoji sun shirya tsaf tare wajen fatattakar ta’addanci, musamman da samun bayanan sirri daga jama’a.
A nasa jawabin, Aminu Ladan Mada ya jajanta rasuwar tsohon Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, tare da yaba jagorancin Soyele wajen yaki da ta’addanci.
Yan ta’adda sun yi barna a jihar Neja
A baya, mun ruwaito cewa wasu miyagun mutane dauke da bindigu sun tafka mummunar barna a jihar Neja, sun kai harin kan manoman a karamar hukumar Mariga.
Rahotanni sun ce 'yan ta’addan sun yi asarar rayukan mutane bakwai, tare da buhunan masara akalla 50, wanda ya jefa jama’a a cikin firgici da jimamin asarar da aka jawo masu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng