'Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Kwamishinan da Ke Yawan Sukar Gwamna a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Kwamishinan da Ke Yawan Sukar Gwamna a Najeriya

  • Ana fargabar tsohon kwamishina wanda ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnan jihar Imo ya faɗa hannun ƴan bindiga
  • Matar Dr. Fabian Ihekweme ta koka kan yadda wasu ƴan bindiga suka tursasa direbansu ya jawo masu mijinta har bakin ƙofa
  • Dr. Fabia, wanda ya yi aiki a matsayin kwamishinan harkokin waje, ya shahara wajen sukar Gwamnatin Uzodinma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Imo - Ana fargabar ƴan bindiga sun yi garkuwa da tsohon mutumin gwamna Hope Uzodinma wanda ya koma yana sukarsa daga baya.

Dr Fabian Ihekweme ya yi aiki a gwamnatin Uzodinma a matsayin kwamishinan harkokin ƙasashen ketare.

Gwamna Hope Uzodinma.
Ana zargin ƴan bindiga sun sace tsohon kwamishina a jihar Imo Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

A wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta gani, wata mata da ta bayyana a matsayin matar Ihekweme ta roki a sako mijinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun sace tsohon kwamishina

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu Bayan Tinubu Ya Kore Ta

Ta koka kan zargin wasu miyagu sun bi diddigin direbanta kuma suka tursasa masa ya yaudari mijinta ya fito ƙofar gida.

“Da farko sun kama direban mijina a ƙofar gida, suka ba shi waya ya kira mijina, da ya fito sai suka tafi da shi,”

- Inji matar.

Ihekweme, wanda ya rike mukamin kwamishina tsakanin 2020 zuwa 2022 a karkashin gwamnatin Hope Uzodimma, ya sauya sheka zuwa PDP daga baya.

Tsohon kwamishinan ya koma sukar gwamna

Tsohon kwamishinan, wanda aka fi sani da Omu, ya kwashe makwanni yana tone-tonen asirin yadda Uzodimma ke mu’amala ta dandalin WhatsApp a jihar Imo.

Leadership ta ce ya yi zargin Uzodimma ya umurci banki da kada ya bari shugabannin kananan hukumomi su cire kudi sama da Naira miliyan 10.

Wannan kalamai ya sa muƙarraban gwamnan jihar Imo suka fara bincike don gano wanda yake ba Ihekweme waɗannan bayanan.

Kara karanta wannan

'Ku ja jari': Abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 ya ba matasa 25 kyautar N7.5m

A wannan mako da muke ciki tsohon kwamishinan ya ce ya gano jami'an tsaro na shirin zuwa su cafke shi, ya buƙaci al'umma su tuhumi gwamna kan duk abin da ya faru da shi.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance game da inda Ihekweme yake, kuma rundunar ‘yan sanda ta yi gum da bakinta.

Sojojin Najeriya sun gwabza da ƴan ta'adda

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar soji ta yi arangama da yan ta'adda masu fafutukar kafa kasar Biyafara a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo kuma sojojin Najeriya sun kashe da dama daga cikin yan ta'addar yayin fafatawar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262