An Kakkaɓo Tarin Ƴan Daba Ɗauke da Makamai Masu Haɗari
- Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta kai samame na musamman a kan ƴan daba da aka fi sani da ƴan sara suka
- A yayin samamen, an kama matasa da dama dauke da manyan makamai da ake zargin suna ta'addanci da su a sassan Bauchi
- Kwamishinan ƴan sanda ya tabbatar da cewa za a gurfanar da matasan da ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Yayin da ake shirin bukukuwan karshen shekara, ƴan sandan Bauchi sun shirya domin samar da cikakken tsaro.
Jami'an ƴan sanda sun kai samame unguwanni da dama a Bauchi kuma sun kama matasa da ake zargin ƴan sara suka ne.
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta wallafa yadda aka kama matasan da ake zargin a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi ram da ƴan daba a jihar Bauchi
Rundunar ƴan sanda ta kai farmaki wuraren da ƴan sara suka ke taruwa a unguwannin jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya biyo bayan yawan kira da ake yi wa ƴan sanda ne a kan yawaitar ƴan sara suka a jihar.
Ƴan sandan sun tabbatar da cewa ƴan sara suka na cikin waɗanda suke barazana ga rayuka da dukiyar al'umma.
"A ranar 24 ga Nuwamba ƴan sanda sun yi samame unguwannin Sale Toro, Kofar Dumi, Fadan Bayak da Wunti.
An kama matasa da ake zargi ƴan sara suka ne guda 16 dauke da makamai masu haɗari yayin samamen.
Ƴan sanda za su cigaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiya wajen kamawa da ladabtar da masu laifi a jihar."
- SP Ahmed Mohammed Wakili
Kwamishinan ƴan sandan jihar ya yi kira ga iyaye kan lura da tarbiyyar ƴaƴansu musamman a wannan lokaci.
CP Auwal Musa Muhammad ya bukaci al'umma da su cigaba da ba ƴan sanda hadin kai wajen kakkaɓe miyagu a jihar.
An kama masu taimakon ƴan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa yan sandan jihar Bauchi sun kama wasu matasa biyu da ake zargi da taimakon ƴan bindiga.
Rahotanni sun nuna cewa matasan suna zama a gari ne suna tura bayanan mutane ga ƴan bindiga domin a yi garkuwa da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng