Shugaba Tinubu Ya Dura a Ƙasar Faransa, Ya Fara Muhimmin Aikin da Ya Kai Shi
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Faris na ƙasar Faransa da yammacin ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024
- Bola Tinubu, wanda ya samu rakiyar uwargidar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ya ziyarci Faransa ne bisa gayyatar Emmenuel Macron
- An ruwaito cewa shugaban Najeriya ya samu kyakkyawar tarba da karramawar soji da jirginsa ya sauka a filin jiragen sama na Orly
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Paris, France - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Paris na kasar Faransa da yammacin jiya Laraba.
Shugaban kasar ya tafi Faransa ne ziyarar aiki ta kwanaki uku domin karfafa alakar Najeriya da ƙasar Faransa.
Shugaban ya samu rakiyar uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin Faransa sun tarbi Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Orly da misalin karfe 5:10 na yammacin ranar Laraba agogon Najeriya.
Jami'an tsaron kasar Faransa sun tarbi Bola Ahmed Tinubu da cikakkiyar karramawar soji, wanda ke nuna farkon ziyarar da ya kai ta kwanaki uku.
Sai dai rahotonni sun ce shugaban Najeriya zai fara tarurrukan da aka tsara masa a wannan tafiya yau Alhamis, 28 ga watan Nuwamba, a gidan tarihi na Les Invalides.
Shugaba Tinubu zai fara taruka yau Alhamis
Ana sa ran shugaban ƙasar Faransa, Emmenuel Macron, da uwargidarsa, Brigitte Macron za su tarbi Mai girma Bola Tinubu cikin girmamawa a gidan tarihin.
Bayan nan kuma akwai liyafar ban girma da aka shirya a Palais de l’Élysée, domin karrama shugaban Najeriya, Channels tv ta kawo.
Shugabannin biyu za su halarci wani zama da ‘yan kasuwar Faransa da Najeriya, kuma kamfanoni masu zaman kansu a fannin bunkasa tattalin arziki za su hallara.
Kashim Shettima ya tafi kasar Cote d'Ivoire
A wani rahoton, an ji cewa Mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima, ya tafi Cote d'Ivoire domin halartar taron SIREXE na shekarar 2024.
Sanata Kashim Shettima zai halarci taron ne domin ya amsa gayyatar da mataimakin shugaban ƙasar Cote d'Ivoire, ya yi masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng