Gwamna Ya Rikita Ma’aikata da Farin Ciki, Sun Fara Karbar Albashin N85,000

Gwamna Ya Rikita Ma’aikata da Farin Ciki, Sun Fara Karbar Albashin N85,000

  • Ma'aikata a jihar Rivers sun cika da farin ciki bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya fara biyan mafi karancin albashi
  • Gwamnan ya biya daukacin ma'aikatan jihar mafi karancin albashin N85,000 kamar yadda ya yi alkawari a baya
  • Shugaban kungiyar ma'aikata reshen jihar, Chukwuma Osunna ya tabbatar da fara biyan albashin, ya godewa Gwamna Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya cika alkawari ga ma'aikata bayan fara biyansu mafi karancin albashi a Rivers.

Ma'aikatan jihar sun barke da murna bayan fara karbar albashin N85,000 na watan Nuwambar 2024 da muke ciki.

Gwamna ya fara biyan N85,000 ga ma'aikata
Ma'aikatan jihar Rivers sun fara karbar albashin N85,000 da Gwaman Fubara ya yi musu alkawari. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Instagram

Ma'aikatan Rivers sun fara karbar albashin N85,000

Shugaban kungiyar ma'aikata reshen jihar Rivers, Chukwuma Osunna shi ya tabbatar da biyan albashin a hira da Tribune ta bibiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osunna ya ce Gwamna Fubara ya cika alkawarin da ya dauka a yau Laraba 27 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnati na cikin alheri dumu dumu, gwamna ya fara biyan N72000

"Gwamna ya cika alkawari da ya dauka, a yau 27 ga watan Nuwambar 2024 ina tabbatar muku da cewa ya biya N85,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata."

- Chukwuma Osunna

Fubara: Ma'aikatan Rivers sun godewa gwamna

"Dukan ma'aikatan jihar suna cikin farin ciki marar misaltuwa kan wannan abin kirki da aka yi."
"Mun yi zama har da shugaban ma'aikata, mun ga albashin ya tsaru yadda ya kamata, a yau an fara biyan albashin zuwa gobe wasu bankuna suma za su biya."

- Chukwuma Osunna

Ma'aikata da dama a jihar sun nuna jin dadinsu inda suka yi alkawarin zage damtse yayin da karin albashin ya kara musu karfin guiwa, cewar Arise News.

Gwamna Fubara zai biya N85,000 a Rivers

A baya, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya kere N70,000, ya amince da N85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin Ribas.

Shugaban ma'aikatan jihar, George Nwaeke ya ce gwamnan ya amince da sabon albashin ne yayin ganawa da ƴan kwadago.

Kara karanta wannan

Jigawa ta yi zarra tsakanin jihohi, ta yi wa ma'aikata gata bayan ƙarin albashi

Fubara ya zama gwamna na biyu bayan Babajide Sanwo-Olu na Lagos da ya kai albashi N85,000, sama da na gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.