'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Hafsan Sojojin Najeriya Ya Ɗauki Alkawari a Zauren Majalisa
- Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya sha alwashin dawo da zaman lafiya idan aka tabbatar da shi a matsayin hafsan sojin ƙasan Najeriya
- Mukaddashin hafsan sojin ya ɗauki wannan alkawarin ne a wurin tantancewa a gaban kwamitin haɗin guiwa na majalisar tarayya
- Ya bukaci haɗin guiwa tsakanin Najeriya da kasahen makota domin murkushe duk wata barazanar tsaro a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Muƙaddashin hafsan rundunar sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya sha alwashin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.
Oluyede ya ce idan har aka tabbatar da naɗinsa a matsayin cikakken hafsan sojojin ƙasa, zai baje kwarewarsa wajen dawo da zaman lafiya a ƙasar nan.
Hafsan soji ya shirya mukushe ƴan bindiga
Mukaddashi hafsun sojan ya yi wannan kalamai ne yayin da kwamitin haɗin guiwa na majalisar tarayya ya fara tantance shi yau Laraba, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada cewa matsalar tsaron Najeriya na bukatar kowane ɗan kasa ya ba da gudummuwa a haɗa karfi da karfe wajen murkushe duk wata barazana.
Ya kuma yi kira da a kara danƙon haɗin guiwa tsakanin Najeriya da maƙwabtan ƙasashe, sannan hukumomin sojoji su kara haɗa kai su yi aiki kafaɗa da kafaɗa.
Kalaman Oluyede a zauren majalisa
"Shekaru 30 kenan ina aiki a gidan soja, na yi aiki a matakai daban-daban na tsaro tun daga ƙarami zuwa babba, don haka a shirye nake da wannan matsayi da za a tantance ni a yau.
"Ba zan nesanta kaina daga nasarori da koma bayan da aka samu a rundunar soji a ƴan shekarun da suka wuce ba, amma ina ganin naɗa ni a matsayin hafsan soji wata dama ce ta kawo sauyi."
"Idan aka tabbatar mani da wannan matsayi, na yi alƙawarin zan sadaukar da kaina na yi duk mai yiwuwa wajen sauke nauyin da ya rataya kaina."
- Olufemi Oluyede.
Sojoji sun yi wa ƴan ta'adda rubdugu
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin rundunar hadin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a Borno.
Jami'an tsaron sun kashe ƴan ta'adda 15 bayan an yi musu rubdugu ta sama da ƙasa a yankin Guzamala na jihar da ke Arewa maso Gabas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng