Kano: Kotu Ta Yi Zama a Shari'ar da Ake Yi kan Hana Kananan Hukumomi Kudinsu
- Babbar Kotun jihar Kano ta tsaida lokacin yin hukunci kan korafin da aka shigar game da kudin kananan hukumomi
- Kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE) ta shigar da karar CBN da wasu kan neman hana kananan hukumomin hakkinsu
- Daga cikin wadanda ake kara akwai Ministan shari'a da hukumar RMAFC da wasu bankunan 'yan kasuwa da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Babban kotu a Kano ta yi zama kan shari'ar da aka shigar kan kudin kananan hukumomin jihar.
Kotun ta tanadi hukunci kan korafin da kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE) ta shigar kan bankin CBN.
An maka CBN a kotu kan kananan hukumomin Kano
Daily Trust ta ce NULGE ta shigar da karar kan babban bankin CBN game da rike kudin kananan hukumomin jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda ke korafi akwai shugaban kungiyar NULGE da Ibrahim Muhd da Ibrahim Uba Shehu.
Sauran sun hada da Ibrahim Shehu Abubakar da Usman Isa da Sarki Alhaji Kurawa da Malam Usman Imam.
Masu korafin ta bakin lauyansu, Bashir Yusuf Muhammad sun bukaci kotun ta dakatar da masu neman hana kudin ga ƙananan hukumomi.
Daga cikin wadanda ake kara akwai Ministan shari'a da hukumar RMAFC da ƙananan hukumomi 44 da bankin UBA da Access da wasu bankuna kasuwanci guda shida a Najeriya.
A bangarensa, lauyan CBN, Ganiyu Ajape ya bukaci kotun ta cire sunan bankin daga cikin wadanda ake kara saboda rashin dacewa da hujjoji.
Daga bisani, alkalin kotun, Mai Shari'a, Ibrahim Musa Muhammad ya dage shari'ar ya ce za a sanar musu da lokacin yanke hukunci.
Kudin kananan hukumomi: Kotu ta ba da umarni
Kun ji cewa babbar kotun Kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Musa Muhammad, ta ba da umarni kan riƙe kuɗin ƙananan hukumomin jihar Kano.
Kotun ta bayar da umarnin hana hukumomin gwamnatin tarayya yin katsalanda ga kuɗin da ake ba ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano duk wata.
A cikin umarnin kotun mai ɗauke da kwanan watan 4 ga watan Nuwambar 2024, alƙalin ya ba masu shigar da ƙarar izinin miƙa takardun kotu a ofisoshin Akanta Janar na tarayya, bankin CBN da hukumar RMAFC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng