Majalisar Tarayya Ta Ware Gwamna 1 a Arewa, Ta Yaba Masa kan Ayyukan Alheri

Majalisar Tarayya Ta Ware Gwamna 1 a Arewa, Ta Yaba Masa kan Ayyukan Alheri

  • Gwamna Umaru Mohammed Bago na jihar Niger ya sha ruwan yabo a Majalisar Dokokin Najeriya kan ayyukan alheri da sauran bangarori
  • Majalisar musamman ta ware gwamnan inda ta yaba masa wurin bunkasa harkokin noma a jihar da ke Arewa ta Tsakiya
  • Hon. Babajimi Benson shi ya yi wannan yabo yayin zaman Majalisar a jiya Talata 26 ga watan Nuwambar 2024 a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Majalisar Tarayya ta yabawa Gwamna Umaru Bago na jihar Niger kan bunƙasa tattalin arziki.

Gwamna Bago ya samu yabon ne yayin gabatar da kudiri da Hon. Babajimi Benson daga jihar Lagos ya yi a Majalisar.

Majalisa ta yabawa Gwamna kan bunƙasa harkokin noma
Gwamna Umaru Bago na jihar Niger ya sha ruwan yabo kan inganta harkokin noma. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Asali: Facebook

Niger: Majalisar Tarayya ta yabawa Gwamna Bago

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta ce Benson ya bayyana haka ne yayin zaman Majalisar a jiya Talata 26 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya nemo hanyar yakar Lakurawa, ya fadi masu daukar nauyinsu

Hon. Benson ya ce shugabannin kasashen Afirka da dama suna yi masa magana kan bunƙasa noma da Bago ke yi.

Dan Majalisar ya ce yana da muhimmanci a riƙa yabawa kokarin wasu jihohi kan harkokin noma.

"Janar a soja daga Kamaru ya kira ni inda yake yabon Gwamna Bago kan bunƙasa harkar noma kuma bai san shi ba."
"Gwamna Bago ya yi kokari wurin bunkasa noma da sauran bangarori ciki har da bangaren addini."

- Hon. Babajimi Benson

Yadda Gwamna Bago ya shiryawa noma a Niger

Har ila yau, Hon Abdullahi Saidu daga Niger ya ce jihar ta zama a kan gaba wurin inganta harkokin noma da kiwo, cewar Tribune.

Hon Saidu ya ce Gwamna Bago ya ware hantsi 250,000 domin bunkasa noma da kuma kayan aiki na zamani a jihar.

Gwamna Bago ya inganta harkokin noma

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da noma da kayan aiki na zamani a damunar bana inda ake fatan samun kayan abinci mai tarin yawa.

Kara karanta wannan

'Sharrin Kwankwaso ne': Dan Majalisar NNPP ya yi martani kan shirin tumbuke shi

Gwamna Umaru Muhammad Bago ya fara shirin noman ne a kokarinsa na samar da abinci da zai wadata yan Najeriya sosai.

Umaru Muhammad Bago ya bayyana cewa amfani da kayan aikin noma na zamani zai taimaka wajen rage hasara da ake yi sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.