Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda da Dama yayin Wani Artabu
- Dakarun sojojin rundunar hadin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a Borno
- Jami'an tsaron sun kashe ƴan ta'adda 15 bayan an yi musu rubdugu ta sama da ƙasa a yankin Guzamala na jihar
- Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa a hannun ƴan ta'addan masu tayar da ƙayar baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar hadin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) da ke ƙarƙashin sashe uku na Monguno a Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 15.
Dakarun sojojin sun kashe ƴan ta'addan ne a wani samame da suka kai a garin Kukawa na jihar Borno.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar MNJTF ta fitar, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda a Borno
Rundunar hadin-kan ta bayyana cewa harin, ɗorawa ne kan nasarorin da aka samu kan ƴan ta'addan ISWAP a yankin waɗanda aka raunata a fafatawar da ake yi da su.
Sanarwar ta bayyana cewa sashen sojojin sama na rundunar ya farmaki ƴan ta'adda masu ɗauke da makamai da ke kan babura a Guzamala, inda suka yi munanan raunuka.
Sojojin ƙasa sun hallaka ƴan ta'adda 15 tare da kama ɗaya da rai yayin da suka yi yunƙurin tserewa bayan sun samu raunuka.
An ƙwato makamai masu tarin yawa
A yayin samamen, dakarun sojojin na MNJTF sun samu nasarar ƙwato makamai masu tarin yawa daga hannun ƴan ta'addan.
Daga cikin makaman akwai, bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai, babbar bindigar RPG guda ɗaya da harsasan Shilka guda 152.
Sojoji sun sheƙe kwamandan ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji sun hallaka wani kwamandan ƴan ta'adda Munzur Ya Audu.
DHQ ta kuma sanar da cewa dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 114 tare da cafke guda 238 a cikin mako ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng