Sanata Ndume Ya Gwabza da Shugabannin Majalisa kan Kudirin Harajin Tinubu

Sanata Ndume Ya Gwabza da Shugabannin Majalisa kan Kudirin Harajin Tinubu

  • Majalisar dattawa ta shiga hargitsi yayin da aka zo bayani kan kudirin harajin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke neman kawowa
  • An gayyato shugabannin FIRS da na DMO domin su yi bayani ga majalisar a kan manufofin kawo kudirin haraji da shugaba Tinubu ya yi
  • Sai dai Sanata Ali Ndume da Abdul Ningi sun nuna kin amincewa da gayyatar da aka yi musu inda suka ce ya saba doka aikin majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An samu hargowa a majalisar dattawa kan kudirin harajin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hakan ya faru ne yayin da Sanata Bamidele ya bukaci gayyatar shugabanin FIRS da DMO zuwa majalisar su yi bayani.

Ali Ndume
An yi hargowa a majalisa kan kudirin haraji. Hoto: Barau I. Jibrin|Ali Muhammad Ndume
Asali: Facebook

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Sanata Ali Ndume da Abdul Ningi sun ce hakan ya saba dokar zaman majalisar.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar sanata, Kawu Sumaila ya karbi mukaminsa, an yi zargin siyasa a nadin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume ya buga da Barau Jibrin a Majalisa

Sanata Ali Ndume ya soki damar da aka ba shugabannin FIRS da DMO na shiga majalisa kan kudirin harajin Tinubu yayin da Barau Jibrin ke jagorantar zama.

"Kudirin haraji abu ne mai muhimmanci da bai kamata a yi gaggawa a kansa ba. Yan Najeriya na kallon abin da muke yi."

- Ali Ndume

Duk da korafin Ndume, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ba shugabannin FIRS da DMO damar shiga majalisar.

Vanguard ta wallafa cewa daga nan Ali Ndume ya fusata inda ya ke cewa Sanata Barau ya yi watsi da maganarsa ne saboda yana jagorantar majalisar.

"Za ka iya dakatar da ni daga magana amma ka sani cewa zan cigaba da magana a madadin talakawan Najeriya."

- Ali Ndume

A daya bangaren, Sanata Abdul Ningi ya ce ya kamata shugabannin FIRS da DMO su tattauna da yan kwamitin majalisa kan haraji ne ba wai su shigo musu ba.

Kara karanta wannan

'Sharrin Kwankwaso ne': Dan Majalisar NNPP ya yi martani kan shirin tumbuke shi

Zaman yan majalisar ya nuna yadda za a iya samun rabuwar kai a kan kudirin haraji da Bola Tinubu ya aika musu.

Ndume ya samu goyon baya a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa mutanen Kudancin Borno sun jaddada goyon bayansu ga Ali Muhammad Ndume kan sukar sabon kudirin haraji.

Sanata Ali Ndume ya sha suka bayan ya bayyana a fili cewa ba zai goyi bayan kudirin haraji da gwamnatin Bola Tinubu ta aiko majalisa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng